KEBBI, NIGERIA - Baya ga batun aringizon kuri'u da magudin zabe, babban batun da jam'iyar PDP ta fake da shi wajen kalubalantar zaben gwamna da mataimakinsa shi ne batun takardar shaidar kammala karatun mataimakin gwamna Umar Abubakar Tafida.
Jam'iyar PDP ta kalubalanci cewa maiataimakin gwamnan bai kammala makarantar Sultan Abubakar da ke Sakkwato da ya ce ya kammala ba, kuma lauyoyin jam'iyar sun ce sun gabatar da hujjojinsu, akan abin da suke zargi.
Barrister Nura Bello na daga cikin lauyoyin PDP da suka ce sun gabatar da gamsassun hujjoji.
A karshe dai kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin mai shari'a Ikfem Okpe Ofen ta zartar da hukuncin yin watsi da karar da PDP ta shigar gabanta.
Lauyan APC Abdullahi Yahaya SAN ya ce da ma masu shigar da karar ba su da gamsassun hujjoji don haka abin da kotun ta yi shine daidai.
Mun yi kokarin jin ta bakin Jagororin jam'iyar ta PDP ko ‘dan takakar na gwamna, domin jin matsayar su akan wannan hukunci da kotu ta yanke, amma mun samu kakakin jam'iyar Garba Liman wanda ya ce ba su gamsu da wannan hukunci ba kuma za su daukaka kara.
Da ma masu sharhi akan lamurran yau da kullun kamar Farfesa Bello Badah na dora alhakin tankiyar da ake samu wurin zabuka har zuwa kotuna akan su kan su 'yan siyasar.
Yanzu dai a iya cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, domin jam'iyar da ta sha kashi ta ce zata je kotun daukaka kara, in ma ta kama har kotun koli, ko da za ta samu galaba ga korafe-karafen ta, lokaci ne kawai zai nuna.
Saurari açıkken rahoto daga Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna