Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan bindiga suka kai hari wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 29 a jihar Sakkwato da kuma wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutune 3 a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Harin da 'yan bindigar suka kai a garin Soron Gabas da ke karamar hukumar Binji ta jihar Sokoto mako biyu da suka gabata lokacin da rundunar 'yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane hudu, shi ne ya bar baya da kura, inda aka yi ta samun yamutsi tsakanin Hausawa da Fulani da ke makwabtaka da juna, har aka sami salwantar rayuka Ashirin da tara.
Shugaban karamar hukumar ta Binji, Umar Dan Habi Tudun Kose, ya ce lamarin ya faru a mazabun Soron Gabas da Soron Yamma inda baya ga mutane 29 da suka rasa rayukan su, haka kuma anyi garkuwa da wasu mutane 30.
Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu, a lokacin da yake jajantawa al'ummomin, ya ce ba da jimawa ba wannan matsalar ta cin zarafin al'umma da 'yan bindiga ke yi za ta zama tarihi.
A jihar Kebbi ma a cikin daren Talata wayewar garin ranar Laraba, 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Kanzanna da ke karamar hukumar Bunza inda suka hallaka wasu mutane suka tafi da wasu.
Shugaban karamar hukumar Bunza Alhaji Umar Ahmad yace 'yan bindigar sun kashe mutum uku kuma sun tafi da wasu mutum biyu.
Akan haka ya nemi shigowar gwamanati domin daukar matakan kare sake aukuwar irin wannan harin.
Tuni da Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Kebbi, CP Chris Aimono Wane ya ziyarci kauyen ya kuma jajantawa jama'ar.
Kwamishinan ya yi Allah wadai da wannan aika-aikar tare da bayar da tabbacin cewa rundunar 'yan sanda tana bibiyar lamarin domin kokarin 'yanto mutanen da aka sace.
Lamarin rashin tsaro dai na ci gaba da addabar jama'a a Najeriya musamman a arewacin kasar, duk da yake mahukunta na cewa suna kokarin shawo kan matsalar.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna