Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kararrakin Zabe Ta Yi Watsi Da Karar Da Tsohon Gwamna Matawalle Ya Shigar


Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)

Yayin da'yan Najeriya ke dakon soma jin sakamakon kararrakin zabukan gwamnoni dake gaban kotunan sauraren kararrakin zabe, babbar jam'iyar adawa ta PDP ta fara samun galaba.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Zamfara mai zamanta a Sakkwato ta yi watsi da karar da tsohon Gwamanan jihar Zamfara Bello Muhammad Mutawalle na jam'iyar APC ya shigar a kan zaben Gwamna Dauda Lawal Dare na jam'iyar PDP.

Karamin ministan tsaro na Najeriya kuma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Mutawalle na daga cikin gwamnonin da suka sha kasa a zabukan gwamna da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris na shekara 2023, inda ya kalubalanci zabe da ayyana gwamna Dauda Lawal Dare na jam'iyar PDP a zaman halataccen zababben gwamna.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin mai shara'a Cordilia Ogadi, ta kori karar da Bello Mutawalle na jam'iyar APC ya shigar saboda rashin cancantarta.

Lauyan mai kariya na daya wato Gwamna Dauda Lawal Dare, Chief Solomon Akuma SAN, ya ce hukuncin da kotun ta yi yayi daidai.

"Hukuncin ya yi, hujjojin da aka bayar masu nagartattu ne, gaskiyar doka ta yi aikinta. Wannan hukuncin zai kara karfafa dimokradiyar mu, domin hukumar zabe ta san cewa abubuawan da take yi daidai ne, kuma duk masu son kalubalanci ayyana dan takarar da ya ci zabe, sai sun shirya"

Shi kuwa lauyan mai shigar da kara, wato tsohon Gwamna Bello Mutawalle na jam'iyar APC Usman Ogwu Sule SAN, ya ce sun yi kokarin nunawa kotu hujjojin su na cin zabe.

"A zaman mu na masu shigar da kara mun nunawa kotu takardun da na hukumar zabe ne masu nuna cewa mun ci zabe, kuma mun yi kokarin nunawa kotun akwai kananan hukumomi, inda ba'a kammala zaben ba, yanzu da wannan hukuncin zamu hadu da mai shigar da kara domin daukar mataki na gaba, domin shigar da kara da yin shari'a suna cikin tsarin zabe don haka ne ma doka ta tanadi a kafa kotunan sauraren kararrakin zabe"

Bayan hukuncin da aka yi na Gwamnan jihar Zamfara akwai sauran kararraki dake gaban kotuna da ake dakon a saka ranakkun yanke su, abinda masu lura da lamurran yau da kullum kamar Farfesa Bello Badah ke ganin cewa da ma 'yan siyasa su ke hana a yi zabe kuma su ke tafiya kotuna.

Yanzu dai lauyan na jam'iyar APC ya ce suna da saura dama biyu a gaba kuma wanda ya shigar da karar zai gaya musu abinda za su yi a gaba domin yana jin cewa fashi ne akayi masa a zaben da gudana da kaddamar da wani ba shi ba a zaman gwamna.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Kotun Kararrakin Zabe Ta Yi Watsi Da Karar Da Tsohon Gwamna Matawalle Ya Shigar.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG