Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kebbi: Iftila'in Ruwan Sama Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 4 Tare Da Ruguza Gidaje Da Yawa


Ibtala'in Ruwan Sama
Ibtala'in Ruwan Sama

Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da ruguza gidaje masu yawa, a jihar Kebbi da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Yanzu haka dai mahukunta na kan daukar matakan taimakawa wadanda lamarin ya shafa da kuma kaucewa sake faruwar haka a gaba, duk da yake matsala ce da ta jima tana ci wa mutane tuwo a kwarya.

Duk da yake an soma samun ruwa a daminar wannan shekarar a makare a wasu jihohin arewacin Najeriya, bayan saukar damina jama'ar wasu yankuna sun soma yin hasara.

Jihar Kebbi dake Arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da masu hasashen yanayi ke nuna cewa ana samun ruwa sama sosai, wasu lokutan ma ana samun ambaliyar ruwa.

Hakan ya soma bayyana a fili sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi, wanda yayi sanadin salwantar rayukan mutane hudu da ruguza gidaje masu tarin yawa a garin Dakingari dake karamar hukumar Suru a jihar Kebbi.

Wani mazaunin garin Aminu Umar Dakingari, yace an jima ba a samu ruwan sama ba kamar haka a yankin.

Dan majalisar Jiha mai wakiltar mazabar Suru/Dakingari Faruk Abubakar Maisudan, yace wannan iftila'i ne kuma mahukunta na kan kai dauki ga wadanda lamarin ya shafa.

To sai dai a cewar Aminu Dakingari wannan matsalar ba sabon abu ba ne, kuma in ba a yi wani abu cikin hanzari ba ruwan zai tayar da garin baki daya.

Sai dai dan Majalisar yace ana kan daukar matakan shawo kan matsalar dake kawo ambaliya a garin na Dakingari.

Tuni dai wani ayari a karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar Suru ya ziyarci yankin domin yin jaje da kiyasta hasarar da iftila'in ya haifar.

Watanni biyu da suka gabata an yi iskar mai karfin gaske da ta yi sanadin ruguza gidaje da yaye rufin gidaje kimanin 200 a garin Zauro, haka kuma wani ruwa da aka yi da ya zo da tsawa yayi sanadin mutuwar mutane uku a garin Alle-Kwara dake gundumar Lailaba a karamar hukumar Argungu.

Bisa ga yadda hukumar kula da hasashen yanayi ke yin hasashe akan yanayin da ke zuwa musamman na lokacin damina, yin amfani da bayanan hukumar tare da daukar matakan kariya ka iya taimakawa wajen kawo saukin matsala idan ta zo.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG