Dakarun Najeriya sun gudanar da wani farmaki na hadin gwiwa a dazukan jihohin Kebbi da Zamfara inda suka samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga.
Samun muhimman bayanan sirri da jami'an sojin suka yi a kan yadda 'yan bindigar suka mamaye kauyen Sangeko na jihar Kebbi ne ya sa aka samu wannan nasarar, ko da yake 'yan bindigar sun yi turjiya amma a karshe sojojin sun hallaka uku daga cikin jigajigansu.
Shugaban karamar hukumar Danko Wasagu a jihar ta Kebbi, Hussaini Aliyu, yace wannan wani ci gaba ne a fafutukar da gwamnati ke yi wajen kawar da ayyukan 'yan bindiga.
A wani farmaki da sojin suka kai a lokaci daya a kauyukan Dansadau, Mai tukunya da Babban Doka, an fafata inda har dan bindigar Dogo Gide ya sha da kyar bayan ya samu raunuka.
A wani bayani da rundunar sojin ta fitar, tace a lokacin farmakin sojoji sun tarwatsa gidan Yau Sarkin Pawa, inda nan ne mafakar Dogo Gide, sannan suka kwato makamai, da babura, da tufafin jami'an tsaro.
Wani mutumin Dansadau yace dama 'yan bindigar na basu wahala gaya, kuma yanzu sun yi farin ciki da samun wannan nasarar.
Ko a makonni biyu da suka gabata sojoji sun samu irin wannan nasara a Sokoto, inda suka hallaka 'yan bindiga masu yawa a dajin Tukandu na karamar hukumar Tangaza.
Masana lamuran tsaro irinsu Dokta Yahuza Getso, na ganin wannan wata manuniya ce kan cewa yanzu shugabannin rundunonin tsaro sun shirya.
Sai dai duk da haka 'yan bindigar sukan mamaye wasu al'ummomi suna cin zarafinsu, kamar yadda wasu mazauna yankunan suka bayyana.
'Yan Najeriya dai sun jima suna fatan ganin lokacin da za a kawo karshen wannan matsalar ta rashin tsaro, ko da za a samu kasar ta kara hawa turbar ci gaba.
Saurari rahoton Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna