SOKOTO, NIGERIA - Iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar da ke jihohin Arewa bakwai na Najeriya, sun kasance cibiyoyi hada-hadar kasuwanci inda a safiya duk ta Allah ana shiga da fice na kayayyaki na biliyoyin Naira wadanda kuma amfani ne na kasashen biyu da ‘yan kasashen.
Sai dai tuni da kasuwanci tsakanin kasashen ya shiga halin lahaula, tare da tafka hasara.
Aliyu Maitasamu Isa shugaban masu noma da fataucin albasa a Najeriya, ya ce Najeriya tana noma tan miliyan biyu na albasa kuma tana fitar da ita zuwa wasu kasashen Afirka amma dole ta Jamhuriyar Nijar ne suke fita zuwa sauran kasashen.
Ya ce amma yanzu rufe iyakokin Najeriya da Nijar ya kawo musu asara ta biliyoyin Nairori.
Ya ce kiyasin hasarar da masu fataucin albasa daga Najeriya zuwa Nijar zuwa Ivory Coast da Ghana da Bennin da wasu kasashe ta haura biliyan biyar.
Su ma masu sana'ar magungunan gargajiya sun ce suna tafka asara sakamakon rufe iyakokin kasashen biyu.
Shugaban kungiyar masu maganin gargajiya a Najeriya Kabiru Muhammad Na Bargu, ya ce suna da daruruwan wakilai masu zuwa daga Nijar suna daukar magunguna domin amfanin mutane, amma yanzu abin ya tsaya cik saboda rufe iyakokin.
Haka dai masu hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen na ci gaba da fuskantar mawuyacin hali saboda wannan matsalar.
Yadda yanayin yake yanzu a iyakokin Najeriya da Nijar ba ‘yan kasuwa kadai ba, har al'ummomi da ke zaune wuraren sun shiga wani mawuyacin hali saboda tabarbarewar harkokin yau da kullum.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna