Lamarin ya faru ne a filin jirgin saman Sarkin Musulmi Abubakar da ke Sakkwato, abin da masana lamurran tsaro ke cewa ba abin mamaki ba ne.
A wani mataki na kara jaddada shirin kawar da miyagun kwayoyi a cikin al'umma hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta kona miyagun kwayoyi da kayan maye na miliyoyin naira da ta kama.
Yayin da wasu al'ummomi dake Arewacin Najeriya ke murnar nasarar da jami'an tsaro ke samu a kan ‘yan bindiga, wasu na nuna fargaba a kan bakin barayi da suke tuhuma na shiga yankunan su.
Fatar da ‘yan Najeriya ke da ita ta magance matsalar rashin tsaro a karkashin sabbin gwamnatoci, na ci gaba da dushewa saboda yadda ‘yan bindiga ke zafafa kai hare-hare daidai lokacin da sabbin gwamnatoci ke kusa da cika kwana arba'in kan mulki.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta ce ta yi kame da yawa na wadanda ke dabi'ar, daidai lokacin da ake kara fadakarwa kan zagayowar ranar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta duniya.
Jama'a na ci gaba da yin tsokaci akan mutumin da aka kashe bisa zargin yin batanci ga Annabi Muhammad SAW a Sakkwato dake Arewa maso Yammacin Najeriya.
‘Yan Najeriya na ci gaba da kokawa akan illolin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da haifarwa wadanda ke kara durkusar da kasar da jama'ar ta.
Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fama da matsalolin rayuwa, wasu gwamnatoci sun himmantu wajen kara lalabo hanyoyin saukaka halin matsi da jama'ar su suke ciki.
A Najeriya, har yanzu ana ci gaba da kai wa wasu al'ummomi hare-hare musamman mazauna yankunan da ke fama da ‘yan bindiga. Wannan na zuwa ne a lokacin da ‘yan bindiga suka afka wasu garuruwa da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, inda suka kashe mutane da dama tare da sace dabbobi masu yawa.
Yayin da wasu al'ummomi a Najeriya ke ci gaba da fuskantar hare-haren da suke tuhumar Fulani barayi ke kai wa, ita kuwa kungiyar Fulani ta kasa ta kara kokawa akan cin zarafi da ta ce ake yi wa Fulani a kasar.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta damu da yadda ayyukan ‘yan ta'adda ke sake kunno kai a wasu yankuna, kuma ba za ta yarda a ci gaba da salwantar da rayukan jama'a tana kallo ba.
Ana ci gaba da samun salwantar rayukan mutane sanadiyar aiyukan ‘yan bindiga a Najeriya, duk da fatan da ‘yan kasar ke yi na samun saukin matsalar tsaro bayan kalaman sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Suran 'yan mata biyu daliban makarantar sakandaren birnin Yawuri uku da aka sace a watan Yunin 2021 sun shaki iskar ’yanci ranar Alhamis, bayan shafe kwanaki 707 a hannun masu garkuwa da mutane.
A wani al'amari da ya girgiza mutanen Karamar Hukumar Isa da ke jihar Sokoto, wata fashewar tukunyar gas ta hallaka mutane biyar baya ga wadanda su ka ji munanan raunuka.
La'akari Da yadda wasu al'adu ko dabi'un al'umma a wasu yankunan Najeriya suke kara kawo matsin a rayuwa musamman ga marasa karfi daga cikin al'umma, gwamnatin jihar Sokoto take kokarin haramta yin almubazzaranci a lokacin bukukuwa.
A Najeriya har yanzu ana samun salwantar rayukan jama'a sanadiyar hadarin kwalekwale duk da matakan da mahukunta ke cewa suna dauka na magance irin wannan matsalar.
Yayin da ya rage kasa da mako uku sabbin shugabanni su karbi ragamar mulki a Najeriya, malaman addini na ganin akwai bukatar a daura shugabannin bisa ga tafarkin da za su samu nasarar shugabanci.
Matsalar rashin tsaro na sake waiwayo wasu yankunan arewa maso yammacin Najeriya duk da yake a baya an dan fara samun sauki.
Yaran da suka rasa iyayensu a rikicin boko haram, a gabashin arewacin Najeriya da wasu daga Sokoto sun kwashe shekaru biyar suna samun kulawa a dukkannin bangarorin rayuwa, daga neman ilimi daga matakin firamare har zuwa jami'a da kuma bangaren koyon sana'o'in hannu.
Samun ‘yantar da dalibai mata hudu daga cikin sauran goma sha daya ‘yan makarantar birnin Yauri da suka rage a hannun masu garkuwa da mutane, alama ce da ke nuna ana iya kubutar da sauran daliban.
Domin Kari