Duba da yadda illolin sauyin yanayi ke barazana ga kasasshen duniya duk da fadi-tashin da suke yi wajen magance su, masana harkokin kare muhalli na ganin akwai bukatar mahukunta su sake sabon lale wajen tunkarar lamarin.
Wannan na zuwa ne lokacin da wasu kasashen ke fama da matsalolin sauyin yanayi, kamar ambaliyar ruwa da fari da sauransu.
Yanzu haka wasu kasashen duniya kamar Girka, Brazil, Bulgaria, Pakistan da sauransu, na fama da matsalolin da ambaliyar ruwa ta haifar, abin da akasarin masana suka alakanta ga illolin sauyin yanayi.
A Najeriya ma, wasu yankuna sun fuskanci irin wadannan matsalolin na sauyin yanayi kamar yadda ruwan sama ya yi sanadin salwantar rayuka a Jihar Kebbi da yadda zaizayar kasa ta hallaka wasu mutane a Abuja da dai wasu matsaloli a wasu sassan kasar.
Da dadewa ne kasasken duniya ke fadi-tashi wajen daukar matakan magance wannan matsalar ta sauyin yanayi wadda wasu ayukkan da mutane ke yi ne ke rura ta, kamar saran itatuwa barkatai, kona daji da dai sauransu.
Ko a makon da ya gabata shugabannin kasashen Afirka sun hadu a Kenya a kan wannan matsalar ta sauyin yanayi.
Kuma matsayar da suka cimma, ita ce ake sa ran ta kasance matsayar Afirka a taro da aka shata yi na duniya kan sauyin yanayi a watan Nuwanban wannan shekara a hadaddiyar Daular Larabawa.
Sai dai masana muhalli na ganin akwai sahihan hanyoyi da suka fi dacewa a mayar da hankali akan su muddin a na son samun nasarar fafatukar da ake yi a wannan fannin.
Har wayau masana muhalli kamar Dokta Dan Asabe Umar na ganin akwai batun sanya gaskiya ga fafatukar da ake yi kan kare muhalli kafin a samu nasarar ta.
Al'ummomi dai na ci gaba da yin tsokaci a kan yadda za a iya shawo kan wannan matsalar ta sauyin yanayi ko da za a iya tsira ko samun sauki daga illolinta.
Yanzu dai a iya cewa yin amfani da shawarwarin masana kan iya nuna yadda za a samu saukin wannan matsala wadda ke ci gaba da kawo koma-baya ga kasashen duniya, ko akasin haka.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna