Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sanda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar yayin da suke kokarin kubutar da wasu 'yan kasar waje a kamfanin sarrafa tumatir da ke garin Ngaski.
A Najeriya matsalolin rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankulan jama'a inda har su ka fara yanke kauna ko za su fita daga yanayin.
A Najeriya iyalan jami'an tsaron da aka kashe a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar, sun gudanar da zanga zanga.
A Najeriya kididdiga ta nuna adadin masu kwankwadar miyagun kwayoyi ya haura mutum miliyan goma sha biyar abinda ya sa kasar ke sahun gaba ga yawan masu amfani da miyagun kwayoyi.
A Najeriya bisa ga yadda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da wanzuwa kuma duk da kokarin da ake yi ya kasa shawo kan matsalar, ya sa ake ci gaba da lalubo hanyoyi daban-daban ko da za'a samu dacewa.
Hukumar hana fasa kwabri ta damke wasu mutane biyu a jihar Kebbi da suke tuhuma da yanka Jakuna kimanin dubu daya da aka kiyasta kudin su fiye da naira miliyan 42 suka yi safarar naman su.
A Najeriya har yanzu ana ci gaba da samun asarar rayuka masu tarin yawa sanadiyar ayukan ‘yan bindiga.
A Najeriya rikice-rikicen siyasa na ci gaba da daukar hankalin ‘yan kasar daidai lokacin da ake kara matsawa ga shekarar da za'a gudanar da zabubukan shekara 2023.
A Najeriya wasu jama'a na ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata jama'a su bullo da hanyoyin da za su ceto kasar da rayukan ‘yan kasa daga matsalolin da suke neman wargaza kasar tunda gwamnatoci sun kasa saukar da nauyin da ke kansu na aza ta bisa turbar cigaba.
A daidai lokacin da ake sa ran fara dauko dalibai ‘yan Najeriya da yaki ya rutsa da su a Ukraine, wasu iyayen yaran na fatar ganin yaran sun iso lafiya.
Har yanzu dai ‘yan Najeriya musamman na arewacin kasar sun kasa samun mafita daga matsalolin rashin tsaro dake hana su yin bacci da ido biyu a rufe.
A Najeriya Mahukuntan kasar sun ce suna da amannar cewa habaka harkokin wasanni zai taimaka wajen kara samar da hadin kan kasa da wanzar da zaman lafiya da aka jima ana lalaben hanyoyin samun wanzuwarsa.
Jihar Sokoto, na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro baya ga Kaduna, Katsina, Zamfara da Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A Najeriya duk da alkawullan da shugaban kasar Muhammad Buhari ya sha nanatawa na hannunta kasa mai cikakken tsaro ga gwamnatin da zata gade shi, har yanzu jama'a na ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci a yankuna daban daban.
A Najeriya, irin wadannan kungiyoyi su ne suka yi ta fafatuka har suka nemowa kasar ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Tarihi ya nuna cewa a arewacin Najeriya tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, akwai zaunannen tsarin shugabanci wanda daular Usmaniya ta assasa.
Dangin Magajin garin Sokoto Hassan Ahmad Danbaba sun tabbatar da rasuwar sa ranar Asabar bayan gajeruwar rashin lafiya.
A Najeriya al'ummomin da suka fuskanci matsalolin rashin tsaro a baya sun fara kokawa domin matsalar ta soma waiwayowa a 'yan kwanakin nan.
A Najeriya batun cunkoso a gidajen gyara hali ya jima yana daukar hankalin jama'a kuma duk da kokarin da mahukunta ke yi don magance matsalar har yanzu ana samun cinkoso.
Rikice rikicen siyasa na ci gaba da daukar hankalin jama'ar Najeriya daidai lokacin da lokutan gudanar da zabubuka ke kara matsowa.
Domin Kari