Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsaro A Nigeria Ya Ci Gaba Da Tabbarbarewa Duk Da Yawaita Alkawarun Gwamnati


'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

A Najeriya duk da alkawullan da shugaban kasar Muhammad Buhari ya sha nanatawa na hannunta kasa mai cikakken tsaro ga gwamnatin da zata gade shi, har yanzu jama'a na ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci a yankuna daban daban.

A wannan mako ma mahara sun kai farmaki a Sokoto inda suka hallaka mutum hudu kuma suka jikkata wasu.

Lokaci na ta tafiya ga karewar wa'adin gwamnatin mai mulki a Najeriya kuma ga jama'a na ci gaba da fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga, ana samun salwantar rayuka da dukiyoyin jama'a musamman na mutanen arewa abinda kan iya haifar da ayar tambaya akan ko za'a samu cikar alkawullan shugaba Muhammad Buhari na hannun ta kasa mai cikakken tsaro ga gwamnatin da zai mikawa mulki.

A jihar Sakkwato ma dake arewa maso yammacin kasar a wannan karahen mako mahara sun afkawa kauyen sabon garin dole, dake karamar hukumar Goronyo har suka hallaka wasu mutane.

Wani mazaunin garin ya shaida wa muryar Amurka kan abinda ya faru inda ya ce sun far masu ne daddare kuma suka dinga harbin duk wadanda su ka yi karo da su da ba su ma san abun da ake ciki ba. Sun kashe mutane da dama, sun kuma raunata wasu wanda yanzu haka suna asibiti.

Duk yunkurin jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya akan batun ya ci tura.

Amma shugaban karamar hukumar Goronyo Abdulwahab Yahaya Goronyo ya tabbatar da kai harin, sai dai saboda baya garin, yace ba zai ce komai ba sai ya je yaga abinda ya faru.

Kawo zuwa hada wannan rahoto an kira sa fiye daya bai karba kiran ba, kuma an tura masa sako a waya bai mayar da jawabi ba.

Mun kuma zanta da mai sharhi akan lamurran yau da kullum Farfesa Bello Badah ko yake suke kallon kai hare-hare ga jama'a musamman duba da alkawullan shugaba Buhari na samar da cikakken tsaro kafin karewar wa’adin gwamnatinsa, ya bayyana cewa shugaba Buhari yayi alkawarin bada tsaro, kuma ‘yan najeirya sun sa ido suna kan jira. Sha’anin tsaro sai da haddin kai kuma babu haddin kai saboda mutane basu da kwanciyar hankali, ga talauci, rashin aiki da tsadar mai.

Shugabannin kananan hukumomi sune shugabanni mafi kusa ga jama'a, sai dai wasu lokuta wasu sukan kauracewa yankunan su dawo cikin birane, su bar jama'a suna neman agaji har dai in mahara sun kutso yankunan su.

Yankin Goronyo dai yana a gabascin Sakkwato kuma ya taba fuskantar harin da ake ganin na ramuwar gayya ne daga ‘yan bindiga wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Matsalar rashin tsaro dai zuwa yanzu ta dauki rayuka da dama tare da daidaita yankuna da al'ummomi a arewacin Najeriya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG