Duk da yake ana samun rahotannin da ke nuna jami'an tsaro sun hallaka ‘yan fashin daji, amma rahotannin da ke nuna ‘yan fashin dajin sun hallaka jami'an tsaro sune suka fi tayar da hankulan jama'a da kuma nuna yadda sha'anin tsaro ke samun koma baya.
A jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan kisan gilla da ‘yan bindiga suka yi wa jami'an soji da na ‘yan sanda ranar Talatar makon da ya gabata sai ga shi a Talatar wannan mako sun sake hallaka wasu ‘yan sanda shida a wata fafatawa da suka yi a kamfanin sarrafa tumatir dake karamar hukumar Ngaski.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bakin kakakin ta a jihar kebbi SP Nafi'u Abubakar ta tabbatar da kisan jami'an 6.
Wani abu da jama'ar garin suka fada shine an samu labarin za'a kawo harin kwana 3 Kafin aiwatarwa shi.
Masu lura da lamurran yau da kullum kamar farfesa Tukur Muhammad Baba na ganin duk da yake in ana yaki ko wane bangare ana samun salwantar rayuka amma dai akwai ban tsoro kisan masu baiwa kasa kariya.
Hakama kai hari a kamfani irin wannan inda gwamnatin Najeriya ta jima tana neman masu saka jari daga kasashen ketare yana illa sosai.
Masana dai na ganin cewa wannan karin manuniya ce ga gwamnati akan ta kara azama wajen kara kimtsa jami'an tsaro musamman wajen samar musu kayan aiki ingantattu da kuma kwakkwarar horaswa don iya fuskantar kalubalen tsaron kasa da jama'a.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: