Hakan ne ma ya sa ‘yan Najeriya ke ci gaba da nuna yatsa ga masu yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi akan ci gaba da wanzuwar matsalolin duk da illolin da suke kawo wa a cikin al'umma.
Tu'ammuli da miyagun kwayoyi matsala ce da ta jima tana damar da ‘yan Najeriya musamman yadda ake ganinta a zaman daya daga cikin abubuwan da ke ruruta da yawa daga cikin matsalolin da ke yiwa kasar tarnaki.
Wasu jama'a na ganin ko matsalar nan ta rashin tsaro da ta gagari magani, shan kwayoyi yayi tasirin gaske wajen zaburar da ita, baya ga sauran matsalolin da dabi'ar ke haifarwa.
Abubakar Mailato YDO yana cikin ‘yan rajin wanzar da zaman lumana da walwala a cikin al'umma yana ganin cewa akasarin mutane da ke aikata munanan laifuka kaman su fyade, kisa, yankar rago, ko kona mutane, duk sukan aikata su ne bayan sun sha wadannan miyagun kwayoyi saboda cire masu imani da kwayar ke yi.
Wani abu da kan iya daure kan jama'a shine irin yadda matsalar ke ci gaba da wanzuwa kuma gashi mahukumta na bakin aiki na dakile aikata ayukkan da har kididdiga ta nuna yawaitar masu hannu da ga dabi'ar.
Misbahu Idris shine kumandan yanki na hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi mai kula da Jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, ya ce bayyanai ya nuna cewa an samu fiye da kashi goma sha biyu da digo uku na mutane da suke mu'amalla da miyagun kwayoyi, kuma a hakan ba a ma hada da masu shan giya ba kenan.
Wani abu da ke baiwa jama'a mamaki shine yadda matsalar taki ci taki cinyewa duk da wannan kokarin da hukuma tace tana yi.
Binciken Muryar Amurka na nuni da cewa, jama'a na fatar ganin an samu nasarar kawar da duk abubuwan da kan iya yin tarnaki ga ci gaban kasa ba, ta yadda lamurra zasu gudana cikin sauki da walwala, kuma hakan ne ake rasawa a Najeriya, abinda wasu ke ganin ya kamata jama'a su bayar da tasu gudunmuwa a gudu tare a tsira tare.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: