A Najeriya daidai lokacin da wasu al'ummomi ke alhini na rashin jikan Sardaunan Sokoto Hassan Ahmad Danbaba, wasu jama'a na ci gaba da tsokaci akan gudunmuwar masu rike da sarautu ga ci gaban al'ummomin su.
Tarihi ya nuna cewa a arewacin Najeriya tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, akwai zaunannen tsarin shugabanci wanda daular Usmaniyya ta assasa, wanda sarakuna ne ke gudanar da ayukkan ga jama'a a fannoni daban-daban, kamar sarautar Magajin Gari, Magajin Rafi da makamantan su.
Faduwar sarautar Magajin Gari ta kara adadin sarautu masu muhimmanci da suka fadi karkashin daular Usmaniyya kuma ba'a yi su ba.
Sarautar Marafan Sokoto, ita ma ta fadi a shekara ta 2016, kuma har yanzu ba'a yi ta ba, duk da yake a can baya wasu bayanai sun nuna cewa an samu tankiya sanadiyar neman sarautar tsakanin Marigayi Inuwa Abdulkadir da Marigayi Hassan Ahmad Danbaba, abin da ya kawo tsamin dangantaka cikin masarautar Sokoto.
Sai dai wasu na ganin babu tabbas ga wannan batun, kamar yadda wakili a hukumar gudanarwa ta gidan tarihi da al'adu na Waziri Junaidu, Comrade Bello N. Junaidu ya fada, musamman duba da rudani da rasuwar Magajin gari ta zo wa jama'a dashi.
Tarihi ya nuna cewa marigayi Hassan Ahmad Danbaba, shi ne na 14 a jerin wadanda suka rika wannan sarautar.
Kawo yanzu dai ba wanda a fili ya bayyana ra'ayin neman sarautar amma akasarin jama'a na alakanta masarautar Gumbi da kusanci ga sarautar duk da yake ba lallai ne hakan ta kasance ba.
Jama'a dai na ci gaba da kwarara jihar Sokoto don yin ta'aziya ciki har da wakilan shugaban Najeriya Muhammad Buhari karkashin jagorancin Ministan shari'a Abubakar Malami.
Masana dai na ganin cewa da za'a baiwa sarakuna dama a hukumance da za su bayar da gudunmuwa da watakila za ta iya tasiri ga saukaka matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: