A Najeriya matsalolin rashin tsaro na ci gaba da kawo salwantar rayuka da dukiyoyin jama'a musamman a yankin arewacin kasar, abin da ya sa wasu ke ganin matakan da mahukunta ke cewa suna dauka ba su da amfani, domin matsalolin sai karuwa suke yi.
A jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin, gabashin jihar ya jima yana fama da wadannan matsalolin, inda a wasu lokuta ko an ga alamun sauki sai matsalar ta waiwayo.
Yanzu haka al'ummomi da ke karamar hukumar Illela garin da a Najeriya ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, suna fuskantar karuwar matsalolin domin kusan duk safiya sai an samu rahoton kai hari ko an kashe ko an sace mutane.
Ko da yake, hukumomin tsaron Najeriya sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarinsu kuma suna samun galaba, inda a lokuta da dama sukan nemi jama'ar wadannan yankunan da su rika taimakawa da bayanan sirri.
Kauyen Danbar Dikko wani kauye ne wanda akasarin sa duk Fulani ne, a karshen makon da ya gabata jama'ar garin sun tsinci kansu cikin tashin hankali sanadiyar wani hari da aka kai garin wanda suke zargin Hausawa ne suka kai musu.
Mai garin na Dambar Dikko ya ce abin ya zo masu da mamaki domin suna zaman lafiya da Hausawan amma kwatsam sai ga wannan farmakin an kai musu.
Kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya akan batun ya ci tura, sai dai Dan majalisar jiha mai wakiltar Illela ya ce bayanin da ya samu shi ne lokacin da aka fatattaki wasu barayi ne suka ruga a guje zuwa garin aka bisu.
Yanzu dai jagororin al'umma a yankin na ci gaba da neman yadda za'a shawo kan irin wadannan matsalolin yayin da su kuwa jama'ar da aka konawa gidaje da kayayyaki ke ci gaba da neman agaji.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: