Rikice rikicen siyasa na ci gaba da daukar hankalin jama'ar Najeriya daidai lokacin da lokutan gudanar da zabubuka ke kara matsowa.
Wani abu da ke jan hankalin ‘yan Najeriya bai wuce batun shugabancin kasar ba, inda wasu ke ganin ya kamata a yi karba-karba tsakanin yankin kudu da arewa, wasu kuma na ganin akasin hakan.
A Najeriya al'ummomin kasar na cigaba da fuskantar hare-haren ta'addanci daga ‘yan bindiga abinda har sun wasu daga cikinsu sun fara yanke kauna ga kawo karshen matsalolin, kawai suna jiran yadda Allah zai yi dasu.
Matsalolin cin zarafin bil'adama na ci gaba da wanzuwa a sassan Najeriya, ciki har da safara da kuma satar kananan yara. Jami'an tsaron DSS a Najeriya sun ceto wasu yara hudu da aka sace daga arewacin kasar aka sayar da su a yankin kudu.
Da yawan jama'a na dora alhakin koma-bayan kasar ga dalilai mabambanta, da kuma hanyoyin da suke ganin za'a iya samun mafita.
Haren-haren ta'addanci na ci gaba da zama sanadiyar rashin rayuka da dukiyoyin jama'a a Najeriya musamman a arewacin kasar.
"Yanzu har shigar burtu suke yi, su yi shigar mata su saka hijabi, su shiga gari su labe. Kullum abin da ke faruwa kenan." In ji Isa Ambarura.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyoyin fafatuka ke ta faman fadakar da jama'a akan illolin shaye-shayen kayan da ke sa maye.
A Najeriya rikice na kara fadada a cikin jam'iyyar APC mai mulkin kasar duk da yake lokaci sai kara matsawa yake yi ga shirye-shiryen zabukan shekara ta 2023.
Ranar Asabar wani rukuni na daliban da aka sace a makarantar Sakandaren birnin Yauri ta jihar Kebbi ya iso a fadar gwamnatin jihar.
A Najeriya sarakunan gargajiya sun jima suna korafi akan ba su da wani tanadi na aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su wanda za su bayar da gudunmowa ga ci gaban al'umar kasa.
A Najeriya, alamu na nuna cewa akwai yiwuwar a samu saukin matsalolin rashin tsaro a wasu yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga saboda a baya bayan nan ana jimawa ba tare da an kai hari ba a wasu wuraren, sai dai kuma ana fuskantar kananan hare-hare a wasu wurare dabam.
A Najeriya daidai lokacin da shekara ta 2022 ke dab da shigowa wadda ita ce jajibirin shekarar zabubuka a kasar, alamu na nuna wankin hula na neman kai dare ga jam'iyar APC mai mulkin kasar domin ta kasa sasanta rikice-rikice da ke ci gaba da tarwatsa ta.
Jama'a na ci gaba da shiga kunci sanadiyar ayyukan ‘yan bindiga da ke ci gaba da aika- aikar su a jihohi da dama na arewacin Najeriya.
Hauhawar farashin dalar Amurka na ci gaba da kawo babban cikas ga ‘yan kasuwar a Najeriya musamman wadanda ke fitar da kaya zuwa kasashen duniya.
A Najeriya ‘yan bindiga na ci gaba tayar da hankalin jama'a ta hanyar hare-haren ta'addanci musamman a arewa maso yammacin kasar.
A Najeriya alamu na nuna akwai yuwuwar an soma fafatawa don dakile ayukkan ‘yan bindiga a wasu yankunan arewacin Najeriya domin mazauna yankunan sun tabbatar da ganin jami'an soji suna dannawa zuwa inda ake tunanin mafakar ‘yan bindigar ce.
A Najeriya bisa ga yadda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da wanzuwa, duk da kokarin da ake yi na magance su, ‘yan kasar sun soma tunanin cewa ya kamata gwamnati ta kirkiro runduna ta musamman daga cikin jama'ar yankunan da ke fama da matsalolin su kare yankunan su.
A Najeriya nasarorin da kungiyoyin fafutukar kare hakkin yara ke samu na haduwa da cikas domin wasu na yi masu zagon kasa, sai dai kuma kungiyoyin da hukumomin kare hakkin bil'adama sun ce sai sun ga abinda zai turewa buzu nadi.
A Najeriya gwamnonin kasar sun sha alwashin jajircewa ta kowace hanya za'a samu saukin matsalolin rashin tsaro, zasu bi ta don ganin an samu shawo kan matsalolin.
Domin Kari