Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Cunkoso A Gidajen Gyara Hali A Najeriya Ya Zama Babbar Matsala


GIDAN YARI
GIDAN YARI

A Najeriya batun cunkoso a gidajen gyara hali ya jima yana daukar hankalin jama'a kuma duk da kokarin da mahukunta ke yi don magance matsalar har yanzu ana samun cinkoso.

Hakan ya sa wasu ke ganin muddin ba tsaiko aka daina samu ba a haujin shara’a ba to matsalar za ta ci gaba da wanzuwa.

Cunkoson jama'a a gidajen gyara hali a Najeriya abu ne da ya zamowa gwamnatin kasar kashin-bakin-tulu tun ma ba lokacin cutar coronavirus ba, lokacin da ake bukatar rage cunkoson jama'a wuri guda.

Ko bayan kwamitin da gwamnatin kasar ta kafa akan rage cunkoson gidajen gyara hali akwai wadanda dokar kasa ta baiwa damar yin afuwa ga wasu dake zaman kaso, kuma suna aikin su amma dai har yanzu ana samun cunkoson a gidajen gyara hali.

Wasu jama'a na ganin rashin yanke hukumci cikin hanzari na daga cikin abubuwan da ke kawo cunkoson.

Jami'an tsaro na daga cikin masu gabatar kara gaban kotuna, kuma wasu lokuta kotunan sai suyi ta daga kara saboda wasu abubuwa da suka hada da ci gaba da gudanar da bincike yayinda masu jiran shara’a ke ci gaba da zaman jiran shara'a gidajen gyara hali.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya a Sokoto ASP Sanusi Abubakar ya ce ba ko da yaushe ne ake samun tsaiko ba wajen binciken wadanda ake tuhuma lokacin da suke fuskantar shara'a a gaban kotuna.

Bisa ga yunkurin rage cunkoso a gidajen gyara kwanannan sai da Babban Jojin jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya Mai shara'a Muhammad Sa'idu Sifawa yayi bitar wasu kararraki.

Wani abu dake kara cunkoson fursononi shine yadda ba'a zartarda hukunci ga wadanda kotuna suka yankewa hukumcin kisa, abinda wasu ke ganin da ana zartarda hukumcin da watakila zai kawo raguwar aikata laifukan da ke da hukumcin kisa.

Cunkoso A Gidajen Gyara Hali A Najeriya Ya Zama Babbar Matsala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG