Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan Na Yunkurin Hada Kan Matasa Ta Hanyar Bunkasa Wasanni Don Wanzar Da Zaman Lafiya


Sunday Akin Dare, Ministan Matasa da Wasanni
Sunday Akin Dare, Ministan Matasa da Wasanni

A Najeriya Mahukuntan kasar sun ce suna da amannar cewa habaka harkokin wasanni zai taimaka wajen kara samar da hadin kan kasa da wanzar da zaman lafiya da aka jima ana lalaben hanyoyin samun wanzuwarsa.

Hakan ne ma yasa mahukuntan suka fara karkata akalar tunanin amfani da bangaren wajen samun biyan wannan bukatar.

Da jimawa wasu daga cikin rahotannin da ke fitowa daga Najeriya sun kasance na damuwa kuma masu sosa rai kasancewar sun karkata akan yadda ‘yan ta'adda ke cin zarafin jama'a ta hanyar kisa ko garkuwa da mutane da sauran nau'o'i na cin zarafi, kuma duk da kokarin lalabo hanyoyin samun mafita da mahukuntan kasar ke yi.

Yanzu mahukuntan sun ce suna da ammana akan ingancin yin amfani da hanyar hada kan matasa wuri daya ta hanyar bunkasa wasanni don wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

Ministan wasanni na kasar Mr Sunday Dare ya bayar da misali da wani yunkuri da suka yi na hadin guiwa na gwama harkokin wasanni da huldar diplomasiya ta amfani da wasu gogaggun ‘yan wasa.

“Abinda ya bayyana a fili ya nuna cewa wasanni na da karfin gaske a wannan haujin, mun ga tsohon shugaban kasar afirka ta kudu Nelson Madela ya bayyana a fili yana alfahari da gogaggun ‘yan wasa sama da 40, inda yake cewa karfin da ke ga wasanni wajen samar da hadin kai ta hanyar amfani da matasa a samar da zaman lafiya abu ne da ba za'a raina ba.”

Ministan yayi tsokacin ne lokacin da yake duba wani aiki na samar da birni na hada-hadar harkokin wasanni da gwamnatin jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya ke kan samarwa, saboda a cewar gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal suna da yakini akan cewa amfanin wasanni tamkar Nagge ne dadi goma.

Ministan yace wannan aikin duk da yake na jiha ne, amma yazo daidai da tunanin gwamnatin tarayyar Najeriya wajen taimakawa matasa su kasance kodayaushe suna da abin yi a gaban su.

“ Abinda muka gani nan da yake ya kai yadda ake bukatar irinsa a koina cikin duniya, gwamnatin Kasar zata saka shi a zaman daya daga cikin wuraren wasanninta wanda za'a amince a rika yin wasanni na duniya da shi, muna da irinsa a jihar Edo, da Lagos mun ji dadi cewa an farfado da irinsa a Abuja, kuma muna bukatar makamantansu a wannan kasar mai girma wadda ke da yawan jama'a kimanin miliyan 220 musamman duba da kimar da kasa tayi ga idanun duniya a haujin wasanni".

Wasu jama'a dai na ganin muddin za'a dage ayi amfani da abubuwan da aka samar yadda aka tsara a rubuce to watakila za'a iya samun muriyar da aka kudurci a samu ta hanyar aiwatar da wadannan ayukkan ko kuma akasin haka.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG