SOKOTO, NIGERIA - Tun lokacin da kasar Rasha to kaddamar da kai hare-hare akan kasar Ukraine hankulan jama'a suka tashi musamman wadanda ke da ‘yan uwa a can kasar saboda rashin sanin halin da zasu shiga sanadiyar yakin tsakanin kasashen.
Dr. Larai Aliyu Tambuwal mahaifiya ce ga daya daga cikin daliban da ke karatu a kasar ta Ukraine, ta ce tun lokacin da suka ji labarain yakin, suka fara shawarwrin irin matakan da za su dauka don taimakawa yaransu.
Ta ce sun aika wa gwamnati ta tashi tsaye domin ita ce uwar yaran da ke karatu a kasar waje.
Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na da dalibai 73 dake karatu a can kasar ta Ukraine kuma yanzu haka dukan daliban acewar gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal an samu nasarar fitar da su daga Ukraine zuwa Budapest da ke kasar Hungary inda daga nan ne za'a dauko su zuwa Najeriya.
Dr. Larai Aliyu ta ce tun lokacin da tashin hankalin ya soma ba su yi sa'a daya ba su zanta da yaran ba har wannan lokacin da suke fatar ganin dawowar su Najeriya lafiya.
Mun yi kokarin kiran wasu daga cikin daliban sai dai sakon ke fitowa na nuna cewa ba'a samun layukansu watakila saboda sun baro Ukraine ne ko kuma yanayin hanyar sadarwa.
Yanzu dai iyaye na cike da fatar ganin yaran sun dawo hannun su kafin kuma shawarar yadda lamarin karatun nasu zai kasance nan gaba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: