Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Na Da Rawar Da Za Su Taka Wajen Shawo Kan Matsalolin Rashin Tsaro A Najeriya - Masana


Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron karfara kungiyoyin fafutuka a Sokoto
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron karfara kungiyoyin fafutuka a Sokoto

Jihar Sokoto, na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro baya ga Kaduna, Katsina, Zamfara da Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

A Najeriya daidai lokacin da mahukunta ke cewa suna fadi-tashi wajen shawo kan matsalolin da suka dabaibaiye kasar ciki har da matsalar rashin tsaro, su kuwa ‘yan kasar suna ci gaba da lalabo hanyoyin da za su bayar da ta su gudunmowa ko da za'a samu nasarar magance matsalolin.

Hadakar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya na daga cikin wadanda suke ganin ya kamata matasa su farka su shigo wajen fafutukar ceto kasar domin gobensu ta yi kyau.

A Najeriya, masana sun jima suna tsokaci akan matsalolin da ke yi wa kasar tarnaki da dalilan da suka haifar da matsalolin tare da bayar da shawarwari akan abin da suke gani a mafita.

A bangare daya kuwa su kansu hukumomi suna ganin suna nasu kokari wajen samo mafita daga matsalolin ta hanyar wasu ayukka da suke aiwatarwa musamman na shawo kan matsalar rashin tsaro da kuma samarwa jama'a saukin rayuwa, kuma har yanzu kokarin nasu ya kasa magance matsalolin.

Har yanzu dai masanan ba su yi kasa a gwiwa ba wajen bai wa mahukunta shawarwari.

Farfesa Usman Yusuf tsohon shugaban hukumar bayar da tallafin kiyon lafiya a Najeriya yana cikin masu bayar da shawarwari ga mahukumta.

Farfesa Abubakar Abdullahi na Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato yana ganin aza matasa bisa tubalin inganta rayukan su babbar hanya ce ta kamo bakin zaren warware kalubalayyen da suka dabaibaice Najeriya.

Comrade Faisal Salisu shugaban gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya reshen jihar Sakkwato na ganin matasa sune sahun gaba ga kawo sauyin ceto Najeriya daga matsalolin da suka tauye ta, hakan ne ma yasa suka daukar wa kansu dawainiyar aza matasan Najeriya akan turbar da suke ganin zata ceto kasar.

Ambassador Yakubu Abubakar shi ne shugaban kungiyar matasan Najeriya reshen jihar Sakkwato yana ganin cewa...

Ita ma Halima Abubakar Talba daliba a jami'ar Usmanu Danfodiyo tana mai ra'ayin...

Duk wadannan fadi-tashi da ake yi wajen ceto Najeriya daga halin da ta fada, muddin Jama’a za su yi da gaske kuma mahukunta za su gwada aiki da shawarwarin da ake bayar wa da watakila an samu mafita daga matsalolin.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:

Matasa Za Su Iya Taka Rawa Wajen Shawo Kan Matsalolin Rashin Tsaro A Najeriya - Masana - 3'09"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG