Wannan na zuwa ne lokacin da kungiyoyi masu zaman kansu, irin kungiyar kyautata rayukan ‘yan kasa ta ‘salama,’ suka dukufa ga ilmantar da jama'a kan muhimmancin ceto kasar daga wargajewa.
A Najeriya dai mahukumta sun jima suna furta kalamai masu nuni akan makudan kudade da suke cewa suna fitarwa don samar da cigaba a kasa, a fannoni daban daban.
Amma dai kawo yanzu yana da wuya a iya nuna daya daga cikin fannonin da ake cewa ana kashewa makudan kudaden, da kuma cigaban da aka samu.
Hakan baya rasa nasaba da yadda matsaloli suka dabaibaice kasar, kama daga matsalolin rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da makamantan su, abin da wasu ke ganin lokaci ya yi da ya kamata jama'a su yi wa kansu karatun ta natsu.
Gogaggiya wajen fafatuka, musamman a fagen siyasa da shugabanci a Najeriya, Hajiya Naja'atu Muhammad na cikin wadanda ke sahun gaba wajen neman sauyi daga wadannan matsalolin. Ta ce da gangan aka kirkiro ta'addanci, kuma akwai laifin arewa cikin wannan lamarin, don ba za a cuce ka cikin gidanka ba, sai ka yarda a cuce ka. Shi ya sa suka fito da wannan shirin don tallafa wa matasa, ba ta bangaren gwamnati kawai ba, da nufin dawo masu da darajarsu da kimarsu.
Shi ma Shu'aibu Mungadi ya ce sau dayawa, rahotannin da hukumar kididdiga ke fitarwa suna nuna koma baya ga lamura a yankin arewa musamman arewa maso yammacin Najeriya duk da yake wasu jagororin jama'a na kalubakantar rahotannin, to amma masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin ba gardama ya kamata a yi ba, amma ya dace a nemo mafita daga koma-bayan.
Shan miyagun kwayoyi na daga cikin abubuwan da masana suka yi ittifaki akan cewa suna sahun gaba wajen ingiza matasa ga aikata ba daidai ba, kuma hakan na faruwa duk da kokarin da mahukunta ke cewa suna yi wajen magance matsalar .
Misbahu Idris, wanda shi ne kumandan yanki na hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi mai kula da Jihohin Sakkwato Kebbi da Zamfara, ya kara jan hankulan matasa. Ya ce dole ne a hada kai don a shawo kan wannan matsalar kuma a dakile.
Duk wannan fafatukar na da manufar ganin an saita matasa bisa hanyar da za ta magance matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta ciki.
Da yake irin wannan fafatukar ta fadakar da jama'a ba yanzu ne aka soma irinta ba, kuma da yawa jama'a na fatan samun sauyi daga matsalolin da ake fama da su, sai dai lokaci ne kawai zai iya nuna tasirin wannan fadakarwar ko akasin haka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: