Tun dai a watan jiya ne aka yi wa wani kwararren likita mai suna DR Obisike Donald Obi da abokinsa Ezikiel Odoja kisan gilla a gidansa dake rukunin wasu gidaje dake unguwar Abuja.
Alluran rigafin cutar COVID-19 da Amurkan ta sake baiwa Najeriya gudunmuwa na a matsayin wani bangare ne na ci gaba da fafutukar shawo kan annobar da a halin yanzu ta zamewa duniya alakakai.
Gwamnatin Najeriya ta umarci jami'an kula da gidajen gyaran hali a kasar su bindige duk wani mutumin da ya yi yunkurin fasa gidajen yari a ko ina cikin kasar.
Hedkwatar Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce dakarunta na musamman wato Special Forces SF sun ceto wasu mstafiya 26 da yan fashion daji suka sace akan hangar Birnkn Gwari zuwa Kaduna.
Biyo bayan zargin da Bangaren Dr. Ahmad Gummi ya yi cewa Jiragen Yakin Najeriya na jefa boma bomai akan fararen hular da busu san hawa ba balle sauka a yaki da yan bindiga da dakarun kasar keyi a yankin arewa maso yammacin Najeriya, rundunar sojin saman Najeriya ta maida martani game da batun.
Rundunar sojojin saman Najeriya dake aiki a rundunar yaki da yan bindiga a jihar Zamfara, da ake kira Operation Hadarin Daji yanzu haka na can tana luguden wuta a sansanonin yan bindiga a jihar Zamfara.
Ministan Babban birnin tarayyar Najeriya Mallam Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta Coronavirus.
Da farko dai 'yan ta'addan sun nuna turjiya, amma biyo bayan barin wuta ba kakkautawa, ala tilas ba girma ba arziki suka saduda.
Sama da sarakuna dari da goma sha uku ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu a sassa daban-daban na Najeriya cikin shekaru hudu da suka shige. Yayin da kuma wasunsu ma suka rasa rayukansu hade da hadimansu.
Da aka tuntubi rundunar ‘Yan-sandan jihar Zamfara akan wannan batu, Kakakinta DSP Shehu Muhammad ya ce zai bincika.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin Jiragen ruwa na rundunar sojojin ruwa guda dari da ashirin da daya da kuma wani jirgin sama mai saukar ungulu na mayakan ruwan a wani bangare na daukar matakin inganta tsaro a kan teku da kuma cikin kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na wadata mayakan kasar da isassu kuma ingatattun kayan aiki don ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro dake addabar kasar a sassa daban-daban.
“Yawancin hare-hare da ‘yan ta’adda suke kai wa a kasuwanni ne, saboda anan matattar jama’a take, kuma a nan za su kwashi abinci."
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bude wani babban taron kasa-da-kasa kan sha'anin tsaro a babban birnin Najeriya.
Wata cacar-baki ta barke tsakanin hedkwatar tsaron Najeriya da dan Majalisar Dokokin jihar Sokoto, kan harin ISWAP da ‘yan bindiga suka kai jihar.
Mayakan sun mika kansu ne ga rundunar Operation Hadin Kai OPHDK a shiyyar Arewa Maso Gabashin kasar.
Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojojin kasa na Najeriya Janar Farouk Yahya ya bada tabbacin cewa ‘yan bindigan nan da suka kai farmaki makarantar horas da hafsoshin sojojin Najeriya wato NDA za a kamo su kuma za su fuskanci hukunci daidai da abin da shuka aikata.
A hukumance, Amurka ta mikawa Najeriya manyan jiragen yakin nan na zami wato A29 Super Tucano a wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a sansanin sojojin saman Najeriya dake filin jirgin saman birnin Abuja.
Turkiyya ta yi alƙawarin ƙarfafa dangantakarta da Najeriya domin taimaka mata wajen magance matsalar ta'addanci da yaki ci yaki cinyewa a kasar musamman ma aika aikar 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabas.
Domin Kari