Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Boko Haram 120, Wasu 965 Kuma Suka Mika Wuya - Hedkwatar Tsaro


A ci gaba da kokarin kawo karshen aika aikar yan bindiga dadi a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, hedkwatar tsaron kasar tace dakarunta dake aiki a karkashin rundunar OPERATION HADIN KAI  na ci gaba da ragargazar yan ta'addan dake ta kashe mutane ba gaira ba dalili.

Mukaddashin daraktan sadarwa kan arangamar da dakarun kasar keyi a sassa daban daban na Najeriyar, Manjo Janar Bernard Onyeako ya fada cikin wani taron manema labaru cewa a mako uku da suka gabata, dakarun kasar sun kara matsa kaimi wajen afkawa yan ta'addan al'amarin kuma dake haifar da da mai ido.

Janaral Onyeako yace cikin wannan lokaci dakarun sun hallaka kimanin masu ikirarin jihadi sama da dari daya da ashirin sannan aka cafke guda hamsin da ransu, motocin yaki biyar da makamai guda hamsin hade da harsasai masu rai sama da dari biyu.

Rundunar tsaron Najeriyar tace mayakan nata kazalika sun kuma kai wani mummunan farmaki kan yan ta'addan a gabar tafkin Tchadi inda suka kashe gomman yan ta;addan kana wasu karin ashirn da biyar kuma suka fada a ruwan tafkin chadin suka mutu yayin da suke kokarin tserewa daga farmakin

Ank yi wannan arangama ne a Bama, Gwoza, Monguno, Konduga, Damboa, Damasak, Gudumbali da Damasak., Sauran wuraren sune Kukawa, Chibok da Dajin sambisa.

A halin da ake ciki, hedkwatarv tsaron Najeriyar ta kuma bayyana cewa kimanin yan Boko Haram dari tara da sittin da biyar ne sukai saranda tare da iyalansu su dari biyar da hamsin galibi yara a yankunann Gamboru, Tumbumma, Kukawa, Baga, Gwoza, Mallam Fatori, Damboa, Kirta Wulgo, Buni yadi, Gujba, Madiyya duk dake jihohin Borno da Yobe.

Cikin wannan adadi mutum dari da hudu yan bangaren Boko Haram ne tsagin ISWAP Dake da sansani a Marte.

XS
SM
MD
LG