Amma cikin wannan shekara da muke bankwana da ita ta 2021, a wani yanayi na kara tabarbarewar tsaron, yan bindigar na kara maida hankali wajen sace sarakunan.
A zancen da ake yanzu haka ‘yan ta'addan na can naci gaba da yin garkuwa da mai martaba Sarkin Gindiri a jihar Filato har sun tuntubi masarautar suna neman kudin fansa.
Hakanan ma a jihar Imo inda ‘yan bindigar ke gasar sace sarakunan don yin garkuwa dasu, a halin yanzu suna rike da wani babban Badarake.
To ko me yaja hankalin ‘yan ta'addan na afkawa iyayen kasa? Wani masani a jami'ar Abuja, Dr. Faruk BB Faruk na jami'ar Abuja yace ta yiwu ganin masu garkuwan sun san sarakunan na da ni’ima da daraja a wurin mutane da dama wannan ya sa in sun kame su za ayi maza a harhada masu kudin da suke nema.
Air Commodore Baba Gamawa shi kuwa cewa yayi dole ne fa gwamnati ta tashi haikan wajen ganin ta murkushe yadda ake ta sace-sacen mutane haka barkatai, in ba haka ba to ba shakka sai masifar ta hadiye kowa sannu a hankali.
Tun tuni dai masana tsaro irinsu Manjo Janar Yakubu Usman ke kokawa ganin yadda kullum ake kama masu satar mutanen a nuna su ga ‘yan jarida daga nan sai aji shiru, yana mai cewa muddin ana hukunta masu laifin to hakan zai rage barnar.
To amma ‘yan sanda na cewa suna kama masu laifin in sun gudanar da bincike kuma su kaisu kotu daga nan sun gama nasu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Karina: