Babban Hafsan Hafsoshin mayakan Ruwan Najeriya, Vice Admiral Auwal zubairu Gambo ya ce za a tuttura jiragen ruwan sassa daban daban na ruwan kasar domin aikin sa ido da ma sintiri wajen tsare kasar ta ruwa a irin wannan lokaci da Najeriya ke fama da matsalar tsaro iri iri.
Da ya ke wa Muryar Amurka karin bayani dangane da irin rawar da wadannan jirage za su taka, kakakin hedikwatar rundunar sojin ruwan Najeriyar, Navy Commodore Sulaiman Dahun ya ce rundunar na da kwararru kuma gogaggun mayaka, amma karancin kayan aiki ne ke dan ci masu tuwo a kwarya, amma yanzu kam za a fuskanci duk wani kalubalen tsaro a ruwan kasar gadan gadan.
Commodore Dahun ya ce ba ko tantama biyo bayan samun wadannan sabbin jiragen za su taka rawa wajen kara inganta aikin mayakan ruwan musamman wajen tunkarar 'yan fashin teku, masu satar danyen mai da ma 'yan fashin teku.
Gwamnatin Najeriyar, inji kakakin mayakan ruwan, ta sayo sabbin jiragen ne daga kasashen Faransa, Vietnam, Spain da kuma Afirka ta kudu, baya ga kuma wani daya da injiniyoyin rundunar ne suka kera shi daga farko har karshe a cikin kasar.
Mai sharhi kan harkokin tsaro na ruwa, Abubakar Abdulsalam ya ce wannan babban ci gaba ne ga rundunar mayakan ruwan duba da girmar yankunan ruwa da suke aikin tsare kasar, in kuma za a sami kari ma to lalle abu ne da zai kara taimakawa.
wannan dai shi ne karo na farko da gwamnati ta samar wa wata rundunar sojin kasar jiragen aiki sama da dari a lokaci guda a tarihin sojojin kasar.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina: