Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ba Najeriya Karin Allurar Rigakafin Cutar COVID-19


Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard ta ziyarci rumbun ajiyar magunguna na Najeriya
Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard ta ziyarci rumbun ajiyar magunguna na Najeriya

Alluran rigafin cutar COVID-19 da Amurkan ta sake baiwa Najeriya gudunmuwa na a matsayin wani bangare ne na ci gaba da fafutukar shawo kan annobar da a halin yanzu ta zamewa duniya alakakai.

Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard ta ziyarci rumbun ajiyar magunguna na Najeriya inda aka jibge gudunmowar da kasarta ta baiwa Najeriyar, inda babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko na Najeriya Dr Faisal Shu'aib ya marabceta.

Gwamnatin Amurka kawo yanzu ta baiwa Najeriya tallafin da aka kiyasta na sama da dala milyan dari da talatin a fannin alluran rigakafi gudanarwa, da sauran tsarabe tsarabe dake tattare da batun na rigakafin,

Amurkan kazalika ta kuma sa hanu wajen horas da sama da jami'an soji da fararen hula dubu dari biyu wajen shawo kan annobar cutar numfashin da kuma tsarin kandagarki dake da alaka da cutar.

Amurka ta nemi yan Najeriya dasu je a masu allurar rigafin don tsare kansu daga cutar abin da tace zai karfafa ba kawai lafiyar yan kasa kadai ba amma zai ma taka rawa a kokarin da ake na shawo kan cutar a duniya,

Kowane mutum inji Amurkan na da irin rawar da zai taka wajen wajen marawa kokarin da duniya keryi na dakile cutar ta corona, sabodahaka Amurka zataci gaba da aiki tare da ma'aikatar lafiya ta Najeriya da ma hukumar yaki da cututtuka ta kasar wajen ganin bayan cutar corona

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG