Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Sanda Sun Cafke Yaron Da Ya Kashe Mai Gidansa a Abuja


Tun dai a watan jiya ne aka yi wa wani kwararren likita mai suna DR Obisike Donald Obi da abokinsa Ezikiel Odoja kisan gilla a gidansa dake rukunin wasu gidaje dake unguwar Abuja.

Haka kuma aka yi awon gaba da wasu kudadensa na dalolin Amurka, da katin fidda kudi na ATM da akai amfani da su aka zare sama da Naira milyan biyu daga asusun ajiyarsa na banki, da ma wata dalleliyar motarsa ta zamani da ya saya watanni biyar da suka gabata da ma jakarsa ta bulaguro.

Shi dai Dr. Obi wanda ya tsara yin bulaguro zuwa Amurka, an mai kisan gillar ne kwana daya kafin tafiyar, al'amarin da ya jefa mazuna rukunin gidagen cikin zullumi da al’ ajabin abin da ya faru duk ko dab tsaron dake wannan yanki.

Amma cikin wani yunkuri , rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta sami nasarar gano tare da cafke wadanda suka tafka wannan danyen aiki, tuni kuma ta kaddamar da wani gagarumin bincike.

Da yake bayyana wadanda ake zargin a hedkwatar rundunar, kwamishinan yan sandan birnin Abuja CP Babaji Sunday ya ce tun lokacin da abin ya faru kwararrun jami'ai masu gudanar da bincike suka dukufa har sai da aka gano wadanda suka tafka aika aikar.

Wani abin mamaki dai shine babban wanda ake zargin yaron gidan likitan mai masa aikace aikace wato Abdulsalam Ibrahim ne ya gayyato wasu abokansa biyu wato fidelis Ezikiel da Philommen Hussain suka daddaure mutanen biyu suka yayyankesu da wuka har saida suka mutu.

Take kuma suka deddebe kayayyakin likitan, abin kenan ma da ya sa 'yan sandan suka bude bincike inda da zaran an kammalka za a gurfanar dasu gaban kotu don girbar abin da suka shuka.

Da takewa muryar Amurka karin bayani, mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin Abuja DSP Josephine ADE ta ce shi yaron gidan likitan ya aje motar likitan da yai awon gaba da ita ne aka ganta ajiye a wani wuri inda masu bincike na yan sandan dake farin kaya suka sa mata ido, lokacin da Abdul din yazo daukar motar ne kuma aka kama shi.

CP Babaji Sunday kazalika ya kuma nunawa 'yan jaridu karin wasu mutane goma sha biyar da suka kame bisa aika aikar satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makami da kuma satar motoci a babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG