A wannan wata na Nuwamba ne hukumar raya kasashe ta Amurka wato USAID ke cika shekaru sittin da daya da fara kaddamar da bada tallafi ga Najeriya.
Hukumar, wacce ita ce ta farko a duniya da ta dau gabarar fara samar da tallafi ga Kasashen duniya, tun dai daga lokacin da aka kafa ta yau shekaru sittin da daya kenan da suka wuce yayin shugabancin Shugaba John Kennedy na Amurka a wancan lokaci ta fara da Najeriya cikin kasashen da fara taimaka masu.
Akwai dai sama da kasashe dari a duk duniya baki daya da wannan hukumar ke taimaka masu wacce kuma ke aiki da kungiyoyi masu zaman Kansu da ma gwamnatoci na samar da tallafi a bangarori daban daban.
Wasu daga cikin fannonin su ne bunkasa Ilmi, kiwon lafiya, shugabanci na gari da dai sauransu.
A shekaru biyun da su ka gabata sama da dala miliyan dari biyar ne USAID ta kashe wajen samar da tallafi a yankin tafkin Chadi galibi kuma a shiyyar arewa maso gabas, inji mataimakin daraktan dake kula da harkokin Afirka ta yamma a gwamnatin Amurka
Kamar yadda kuma wani datttijo a arewa maso gabas din dake zama tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe, Alhaji Baba Ba'aba (Danmasanin Fika) ke cewa tun daga shekarar alif da dari tara da sittin da hudu, lokacin suna ‘yan makaranta, USAID ke kawo masu tallafi a fannin Ilmi.,
Baba Ba'aba ya ce har yanzu irin wannan tallafin na USAID na ci gaba, musamman ga wadanda tarzomar Boko Haram ta daidaita. Ganin duk kungiyoyi da cibiyoyin da ke samar da kayayyakin jinkai babu kamar USAID.
A wannan shekara kadai USAID za ta kashe sama da dala milyan dari bakwai wajen samar da tallafi ga yan Najeriya.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina: