“Rahoton ya kunshi duk binciken da aka yi kan lamarin, hujjoji, da kuma bahasin da DCP Abba Kyari ya bayar da na sauran mutanen da lamarin ya shafa.” Sanarwar ta ce.
A baya dai gwamnati ta haramta mu’amala da takin zamani samfurin Urea a yankin saboda 'yan ta'adda na amfani da shi wajen hada bama-bamai.
A Najeriya an gudanar da wani gagarumin taro kan matsalolin tsaro da nufin yin bita kan yakin basasar kasar na shekaru uku don ganin Irin darussan da za a iya dauka.
Kafin nadin nasa a matsayin sabon kwamandan wannan runduna ta musamman, Disu ya yi aiki a matsayin kwamandan rundunar aiki da cikawa ta RRS a Lagos.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bikin Ranar Sojoji a matsayin wani abin da ke ci gaba da baiwa 'yan kasa kyakkyawan fata da kwarin gwiwa a hankoronsu na rayuwa cikin zaman lafiya irin na al'umar dake rayuwa karkashin tsari na dimokradiyya.
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci babban malamin addinin Musuluncin nan dake Kaduna Sheikh Dr Ahmad Gumi zuwa ofishinta biyo bayan sanarwar da ta zama sa- in-sa tsakanin shehin malamin da rundunar sojojin Najeriya.
Paparoma Francis ya bayyana takaici kan matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta ya kuma bayyana niyar bada gudummuwa domin shawo kan matsalar.
Daga cikin kayan da aka baje, har da mota kirar Hyundai Kona mai amfani da wutar lantarki, wacce aka hada sassanta a cikin kasar.
A wani yunkurin shawo kan matsalar tsaro dake kara tabarbarewa a gabar tekun Guinea, rundunar sojojin ruwan kasar Ghana ta nemi agaji daga takwararta ta Najeriya don shawo kan matsalar.
A ci gaba da hauhawar kazancewar tsaro a kusan duka sassan Najeriya, babban titin Abuja da ya tashi daga Kaduna zuwa Zariya da kuma garuruwan dake zagaye da yankin da birnin na Zazzau mai dimbin tarihi da muhimmanci a halin yanzu dai na cikin firgici
Manjo Janar Yahaya, ya rike mukamai da dama ciki har da Kwamandan rundunar tsaro ta Briged da kuma mukamin Darekta a kwalejin sojoji ta AFSC.
Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen kara samarwa mayakan ruwan jiragen ruwan yaki da ma sauran kayayyakin aiki, don kara tunkarar matsalar tsaro gadan gadan.
Yayin da wasu sassan Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar tsaro, wasu 'yan bindiga sun kai wani hari da ya yi sanadin mutuwar dakarun Najeriya 11 a jihar Benue da ke tsakiyar arewacin Najeriya.
Sabon sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya fara aiki tare da shan alwashin fuskantar kalubalen tsaro iri-iri da ke addabar kasar, yayin da wadansu lauyoyi ke kalubalantar nadinsa.
An haifi sabon mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba a garin Gaidam da ke arewa maso gabashin jihar Yobe a shekarar 1963.
Hedkwatar rundunar mayakan daman Najeriya tace wani jirgin yakinta Samfurin Alpha Jet ya bace a jihar Borno.
Sojojin saman Najeriya sun fara dakon tallafin coronavirus ga kasashen Afirka 14, domin dakile sake bullar cutar a karo na biyu.
Tun da farko dai jaridar yanar gizo ta Premium Times ce ta fara kwarmata bayanan cewa sojojin Najeriya sama da dari ne suka arce daga filin daga a jihar Borno.
Hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta tabbatar da cewa wani jirginta ya yi hatsari a ranar Lahadi kuma jami'anta 7 sun mutu.
A wasu sabbin farmaki da rundunar "Operation Tura Ta Kai Bango" da ke karkashin rundunar Operation Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram suka kaddamar, hare-haren na kara kassara ‘yan bindigan na Boko Haram.
Domin Kari