Tunda farko dai mai magana da yawun Dr. Ahmad Gummi, Mallam Tukur Mamu ya yi zargin cewa jiragen yakin mayakan saman kasar na jefa boma bomai ne akan fararen hular da basa dauke da makamai a fafatawar da dakarun kasar keyi wajen dawo da zaman lafiya da kuma kauda yan bindiga dadi dake addabar arewa maso yammacin kasar.
Mallam Tukur Mamu wanda na daga cikin tawagar Dr. Ahmad Gummi da suka karrade dazukan arewacin Najeriyar, inda suka gana da yan bindigar don neman sasanci, ya ce an gaya masu cewa ba kan yan bindiga jiragen yakin kai kai hari ba, amma galibi kauyawan da basiji ba basu gani ba ake aunawa.
Dan Iyan na Fika ya ce an nuna masu wasu rijiyoyi biyu da aka makare da gawauwakin fararen hula da suka rasa rayukansu ta irin wannan hari a wani dajin dake cikin jihar Niger a arewa maso yammacin Najeriya.
Saboda haka, Mallam Tukur Mamu ya nemi gwamnati ta dau hanyar sulhu da yan bindigar ta hanyar gano ainihin musabbin wannan Tarzoma don magance shi baki daya.
Da take maida martani, Hedkwatar rundunar mayakan saman Najeriyar ta ce kokadan wannan zargi ne da bai da tushe balle makama da kuma ke nuna wasu mutane basa farin ciki da nasar da ake samu a yaki da yan bindigar.
Kakakin Rundunar mayakan saman Najeriya Air Commododore Edward Gabkwet, ya shaidawa muryar Amurka cewa kafin jiragen yaki su kai hari sai an kalailaice ainihin inda yan ta'addan suke ta hanyoyin tattara bayanan sirri a kimiyance ta yadda ba yadda za a sami wanda basu aka nufa da harin ba.
Air Commodore Gabkwet ya ce su sojojin sama da sauran jami'an tsaro za su ci gaba da aiki har sai sun magance matsalar tsaro a duk Najeriya baki daya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Makaman Da Yan Sanda Suka Kwace Daga Wasu Bata-Gari