Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Abuja Ya Kamu Da Coronavirus


Mallam Muhammad Musa Bello Ministan Abuja
Mallam Muhammad Musa Bello Ministan Abuja

Ministan Babban birnin tarayyar Najeriya Mallam Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta Coronavirus.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ministan Anthony Ogunleye ya sanyawa hanu ta ce run a ranar ashirin da takwas ga wannan wata na Disamba ne ministan ya fara jin alamun cutar, inda ya yi fama da mura da zubar majina.

Take ya mika kansa ga jami'an kiwon lafiya don gwaji inda sakamakon da aka samu yau ya nuna ministan ya kamu da cutar ta Covid-19.

Tuni ministan ya kebe kansa inda likitoci ke ci gaba da kula da shi dan neman lafiya. Sanarwar ta ce ministan na cikin koshin lafiya kuma yana murmurewa.

Ministan Abujan dai ya karbi allurar rigakafin Coronavirus har sau biyu, ya kuma nemi mazauna birnin da suma suje a masu rigakafin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG