Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsaro Na Haifar Da Wata Sabuwar Matsala A Najeriya – Ministan Tsaro


Manjo Janar Bashiri Salihi Magashi mai ritaya (Facebook/Magashi)
Manjo Janar Bashiri Salihi Magashi mai ritaya (Facebook/Magashi)

“Yawancin hare-hare da ‘yan ta’adda suke kai wa a kasuwanni ne, saboda anan matattar jama’a take, kuma a nan za su kwashi abinci."

Ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya ce kalubalen tsaro na haifar da matsalar karancin abinci a sassan kasar.

Janar Magashi ya bayyana hakan ne yayin taron bita da hukumar leken asirin ta rundunar tsaron Najeriya ta shiryawa hafsoshi da ke kula da sha’anin tsaro a ofisoshin jakadancin kasar a kasashen ketare.

Magashi ya kwatanta wannan matsala a matsayin “sabuwar barazana,” lura da yadda take ruruwa, lamarin da ke shafr ayyukan samar da abinci.

Najeriya na fama da aika-aikar ‘yan Boko Haram da ISWAP a gabashin arewacin kasar da kuma ‘yan bindiga dadi da ma rikicin makiyaya da manoma a yammaci da tsakiyar arewacin Najeriyar na haddasa mummunar barazana ga Najeriya a cewarr Janar din mai ritaya.

Kazalika yankin kudancin kasar ma na da nata matsalolin na tsaro da ke shafar ayyukan samar da abinci.

“Yawancin hare-hare da ‘yan ta’adda suke kai wa a kasuwanni ne, saboda anan matattar jama’a take, kuma a nan za su kwashi abinci.

“Bisa wannan dalili ya sa dole ‘yan kasuwarmu da ma su masu sayen kayen suke kauracewa kasuwannin, saboda tsoron a ko da yaushe za a iya far musu.” In ji Alhaji Isa Adamu, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar arewacin Najeriya.

“Saboda haka, duk lokacin da aka ce ba a bude kasuwanni ba, to dole ne za a samu karancin abinci, kuma duk lokacin da aka samu karancin abinci to dole ne za a samu karin ‘yan ta’addan saboda domin dan adama ba zai iya ruwa bai ci abinci ba.”

A dalilin hakan, ministan tsaron Janar Magashi, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su bullo da dabaru don tunkarar wadannan kalubale.

A cewar masanin tsaro, Salihu Mahmud Dantata, akwai bukatar a mayar da hankali a fannin samar da bayanan tsaro.

“Ya kamata al’uma su zo su rika ba da gudunmowa sannan a arika samun hadin kai tsakanin jami’an tsaro. A kuma samu jirage masu sarrafa kansu don dauko bayanai.” In ji Salihu Mahmud.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

Rashin Tsaro Na Haifar Da Wata Sabuwar Matsala A Najeriya – Ministan Tsaro - 2'54"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


XS
SM
MD
LG