Rahotanni daga jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sabon rikici ya barke a tsakanin wasu kabilu biyu dake yankin Donga na kudancin jihar game da batun sake gina watakotu.
Kungiyar Matasan Afrika UPJ ta tattauna akan Dakurun Sojin kasashen waje da ake turawa kasashen Afrika.
Rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce sun kama tare da mayar da fursunonin da suka tsere daga gidan yari a Ekot Ekene.
Dan takarar jam’iyyar Republican a jihar Alabama, Roy Moore, ya shigar da kara kotu, domin hana jami’an zabe na jihar ayyana abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat a zaman wanda ya lashe zaben.
Mutane kimanin 13 ne suka ji rauni a lokacin wannan harin da tun farko masu binciken kasar Rasha suka ce na yunkurin kisan kai ne kawai a birnin St. Petersburg.
Rundunar sojojin AMurka a nahiyar Afirka ta ce wannan lamarin ya faru ne a wani harin da ta kai daga sama tare da hadin guiwar dakarun gwamnatin Somaliya a wajen babban birnin kasar
A bayan fadan da aka gwabza a tsakanin 'yan kabilar Gwari da Hausawa a garin dake bayan garin Abuja, kura ta fara lafawa yayin da Sarkin Bwari yake kiran da a kai zuciya nesa.
Mutane da dama a kasar Ghana sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta cika alkwarin inganta abubuwan more rayuwa a shekarar 2018.
Man Fetur ya fara wadatuwa a gidanjen mai daban daban a jihar Lagas da birnin Abuja bayan da aka shafe kwananki ana ta wahalar man fetur.
Wani bincike da Cibiyar Bunkasa Demokradiya ta yi ya nuna sakacin mahukunta akan kawo karshen yaki da 'yan ta'addar Boko Haram.
Yayin da ake bukuwan Kirsimeti a Najeriya, mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbanjo ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan matsalar karancin man fetir da ke addabar kasar.
Hukumomi a Birnin Melbourne da ke kasar Australia sun ce, mutumin da aka tsare wanda ya ji wa mutane 19 rauni da gangan
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Yemen, ya nuna matukar damuwarsa a yau Alhamis, kan yadda ake kara samun tashin hankali a Yemen
Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu, bayan da wata gobara ta tashi a wasu gidaje da ke dauke da wani wurin motsa jiki a Birnin Jecheon da ke kasar Korea ta Kudu.
Al'ummar Kristoci na Damagaran a Nijar na shirye shiryen bikin Kirisimeti kamar yadda takwarorinsu a duniya suka sa azamar yin shagulgulan a ranar 25 ga Disambar nan na shekarar 2017.
Kamar yadda Rasha ta yi watsi da manufofin Shugaba Trump na Amurka akan sabuwar manufar tsaron kasa da ya gabatar a jiya Litinin 18 ga watan Disambar shekarar nan ta 2017, haka ita ma Kasar Sin ta yi fatali da manufofin da suka jefata cikin wadanda suka zama barazana ga Amurka.
Yanzu haka kasashen Myanmar da Bangladesh sun kammala shirin ganin sun mayar da musulmin Rohingya da yaki ya tilastawa barin gidajensu don ganin an mayar dasu muhallansu.
Mahukunta a jihar Washington sun bayyana cewa matsanancin gudu ne ya kada jirgin nan na Amtrak da ya hallaka mutane tare da jikkata wasu masu yawa.
Kasar Rasha ta fada yau talata cewa, sabuwar manufar tsaron kasa da Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana ba komai bace illa kwadayin mulkin mallaka, wadda kuma ta nuna Amurka bata amince da ra'ayi ko akidar kowa ba sai tata.
Domin Kari