Makonni biyu da wasu kwanaki a bayan da aka kayar da shi a zabe na musamman na cike wata kujerar majalisar dattijan Amurka, dan takarar jam’iyyar Republican a jihar Alabama, Roy Moore, ya shigar da kara kotu, domin hana jami’an zabe na jihar ayyana abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat a zaman wanda ya lashe wannan kujera.
Jiya laraba da yamma Moore ya shigar da kara a kotun jihar, ‘yan sa’o’i kadan kafin a ayyana Doug Jones a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 12 ga watan Disamba da ratar kuri’u dubu 20 da ‘yan kai.
Karar da Moore ya shigar tana zargin cewa ya fadi a zaben ne saboda magudi mai yawa da aka tabka, inda yayi misali da cewa jama’a sun fito fiye da yadda aka yi tsammani a a karamar hukumar Jefferson wadda ta fi yawan mutane a jihar, da kuma wasu ayyukan da yace sun saba da dokokin zabe a rumfuna 20 cikin karamar hukumar.
Jones dai shine dan Democrat na farko da aka zaba daga Jihar Alabama wadda mafi yawan jama’arta ‘yan Republican ne a cikin shekaru 25 da suka shige.
Facebook Forum