Hukumomi a Birnin Melbourne da ke kasar Australia sun ce, mutumin da aka tsare wanda ya ji wa mutane 19 rauni da gangan, bayan da ya abka kan mutanen da ke tafiya a gefen hanya da motarsa, ba shi da wata alaka da wata kungiyar ‘yan ta’adda.
Mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar Victoria, Shane Patton, ya fadawa manema labarai a yau Alhamis cewa, mutumin da ake zargi mai shekaru 32 dan Australia ne amma asalinsa daga Afghanistan ne.
Ya kara da cewa mutumin yana da tarihin yin amfani da miyagun kwayoyi da kuma matsalar tabin hankali.
Wani dan sanda ne da ya tashi a aiki, ya tsare mutumin, bayan da ya abka da motarsa kan jama’a a wuni wuri da ake tsayar da motoci.
Mukaddashin ‘yan sanda ya kuma kara da cewa an kama wani dan shekaru 24 da aka ga yana daukan bidiyon aukuwar lamarin a wayarsa ta salula.
An kuma tsinci wukake a cikin jakar mutumin na biyu.
Wannan lamari ya faru ne a wata babbar hanya da ke cikin Birnin Melbourne yayin da masu tafiya a gefen hanya suke saye-sayen Kirsimeti.
Facebook Forum