Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Kunya Ne Mu Yi Bikin Kirsimeti Cikin Wahalar Man Fetir – Osinbajo


Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osibanjo (Tsakiya sanye babbar riga) yayin da suke rangadin wasu gidajen man fetir a Legas
Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osibanjo (Tsakiya sanye babbar riga) yayin da suke rangadin wasu gidajen man fetir a Legas

Yayin da ake bukuwan Kirsimeti a Najeriya, mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbanjo ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan matsalar karancin man fetir da ke addabar kasar.

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nuna takaicinsa kan yadda za a gudanar da bukuwan Kirsimeti cikin matsalar karancin man fetir.

Osibanjo ya bayyana hakan ne yayin da ya kai wata ziyarar ba-zata a wasu gidajen mai da ke jihar Legas, kamar yadda wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, dauke da sa hanun jami’in yada labaransa, Laolu Akande ta nuna, wacce Muryar Amurka ta samu.

“Abin kunya ne ana bikin Kirsimeti cikin wannan matsanancin yanayi. Ba haka muka so ba, amma na san cewa irin jarumtakar da ‘yan Legas da sauran ‘yan Najeriya ke nunawa, za mu daurewa wannan matsala, mu kuma more bikin na Kirsimeti.” Inji Osinbajo.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma ce, suna daukan matakan da za su kawo karshen wannan matsala.

“Wannan matsala za ta kau nan ba da jimawa ba, ina zagayawa tare da Ministan albarkatun mai a nan Legas domin mu tabbatar da cewa dogayen motoci suna samun daukan kaya daga dukkanin depo.” Mataimakin shugaban ya ce.

Osinbajo ya yada zango ne a gidajen man Oando da na Hayden da ke unguwar Lekki a ranar jajiberin Kirsimeti kamar yadda sanarwar ta nuna.

An kwashe makwanni kusan uku ana wahalar karancin mai a sassan Najeriya, wanda lamari ne da za a iya cewa ya zama al’ada a duk karshen shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG