Kamar dai yadda rahotanni da kuma shaidun gani da ido suka tabbatar, wannan sabon rikicin ya barke ne a Mararrabar Ba’isa dake yankin karamar hukumar Donga, wanda yayi kaurin suna wajen tashe tashen hankula a kudancin Jihar Taraba.
Bayanai dai na cewa rikicin ya taso ne biyo bayan yunkurin sake gina wata kotu dake daura da wani massalaci inda bangarori biyu na kabilun yankin watau Buban da Beyen kowa ke cewa bangarensa ne, da hakan ya jawo tashin hankalin inda har aka samu hasarar rayuka biyu.
Wani mazaunin yankin da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce rigimar ta taso ne kan gina kotu inda bangarorin biyu ke cewa ba zata sabu ba.
Yace,Kawo yanzu mutum biyu sun rasa rayukansu kuma akwai wadanda ke kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka samu.
Kawo yanzu dai, duk kokarin ji daga bakin dan majalisar dattawa dake wakiltar yankin Senata Emmanuel Bwacha wanda aka ce shi ke son sake gina kotun, abun ya ci tura.
Wakilinmu, Ibrahim Abdul'aziz, ya ce, "na yi ta buga masa waya, amma ba’a dauka ba, haka nan kuma babu amsar sakon kada ta kwanan dana aike masa."
To sai dai kuma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, David Misal, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace hankula sun kwanta, kuma a cewarsa ko tuntube babu wanda yayi a tashin hankalin.
Shi dai wannan rikici na zuwa ne yayin da wani tashin hankali ke aukuwa a tsakanin manoma da makiyaya a yankin Lau, inda a nan ma aka samu hasarar rayuka biyu, kamar yadda kakakin rundunar yan sandan ya tabbatar.
Ga cikakken bayani a rahoton Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum