Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rasha Yace Harin Da Aka Kai A St. Petersburg Na Ta'addanci Ne


Shugabn Rasah Vladmir Putin
Shugabn Rasah Vladmir Putin

Mutane kimanin 13 ne suka ji rauni a lokacin wannan harin da tun farko masu binciken kasar Rasha suka ce na yunkurin kisan kai ne kawai a birnin St. Petersburg.

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin yace wata fashewa da aka samu a St. Petersburg ranar Laraba hari ne na ta’addanci.

Putin ya bada wannan bayani ne a yau alhamis a fadar Kremlin a yayin da ake wani bukin raba kyaututtuka ga ma’aikatan Rasha da sukayi aiki a Syria, amman bai bada Karin bayani akan fashewar bam din ba.

Mutane akalla 13 sun ji rauni bayan da wani bam da aka hada a gida ya fashe a wani kanti dake St. Petersburg, amman daga farko masu bincike sunce suna duban lamarin a matsayin yunkurin kisan kai.

Jami’an lafiya sunce babu wanda ya samu raunin da zai iya hallaka shi a wannan lamarin, haka kuma babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG