A yau ne rundunar sojojin Amurka a nahiyar Afrika ta bayyana cewa Wani hari da ta kai ta sama yayi sanadiyyar mutuwar membobin kungiyar ta’addanci ta al-shabbab hudu da kuma tarwatsa wata mota me dauke da bama bamai a kusa da babban birnin Somaliya.
A bayanin da sojoji suka bayar, harin da aka kai a yammacin Laraba kilomita 25 a yammacin Mogadishu ya taimaka wajen hana tashin bama baman da aka hada a mota musamman domin kai wa fararen hula hari a cikin babban birnin na Somaliya.
Bayanin ya kara da cewa rundunar sojojin Amurka a nahiyar Afrika ta tabbatar da cewa ba a samu mutuwar farar hula ko da guda daya ba a harin wanda a ka kai tare da hadin gwiwar gwamnatin Somaliya.
Amurka ta kai irin wannan harin fiye da sau 30 a shekarar da ta gabata, akan kungiyar ta’addar Al-shabbab da wasu kananan kungiyoyin ta’addar masu tasowa wadanda sukeda goyon bayan kungiyar IS.
A ranar Laraba ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon , ta bayyana cewa wani hari da aka kai ta sama a ranar 24 ga watan Disamba a kudancin Somaliya ya kashe 'yan kungiyar Al-shabbab 13 a arewa maso gabas da birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa.
Facebook Forum