Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu 15 suka jikkata bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a babban ginin horar da ‘yan sandan kasar da ke babban birnin Mogadishu a yau Alhamis.
A yau Alhamis, Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya yi watsi da zargin cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na bara.
An gurfanar da mutumin da ya tayar da wani bam jiya litinin a tashar jiragen karkashin kasa na birnin New York a gaban kotu, inda aka tuhume shi da laifin yin barazanar ta'addanci.
Wannan shine hari na biyu da aka kai a kan jami'an tsaro a yankin Waziristan a wannan watan.
Masu jefa kuri’a a Jihar Alabama a nan Amurka suna zaben cike gurbin wata kujerar majalisar dattijan tarayya da kowa ya sanya idanu a kai, domin cike gurbin da Jeff Sessions ya bari lokacin da ya zamo atoni janar.
Yanzu Shugaban Faransa Emmanuel Macron ke jan ragamar yaki da matsalolin sauyin yanayi inda ya tattaro manyan 'yan kasuwa da shugabannin duniya 50 a wani taro a Paris yau talata wanda zai mai da hankali kan habbaka daukan nauyin kawar da sauyin yanayi.