Ana cigaba da neman hanyoyin warware yaki da kungiyar ta’addar Boko Haram da ke chanza salon yaki da addabar arewa maso gabashin Najeria. Cibiyar Bunkasa Dimokradiya (CDD) ta hada wani taron hadin giuwar kungiyoyin farar hular Nijar da Najeriya, domin Muhawara akan rahotanin binciken da wasu cibiyoyin nazarin cigaban al’umma suka gudanar a Najeriya kan matsalolin da suka biyo bayan rikicin Boko Haram.
Ferfesa Jibiril Ibrahim na Kugiyar CDD ya bayyana cewa irin kashe kashen da ake yi a Najeriya abin mamaki ne, inda mafi yawancin wuraren da rikici ya barke wa, mafi yawancin shuwagabanin garuruwan sun gudu sun bar garin a lokacin da ake ta rikice rikice a garuruwan.
Jibril ya ce a Najeriya yanzu akwai yara milliyan sha uku waddanda basa zuwa makaranta suna almajiranci irin wanda ya sabawa yadda aka yi da, inda ake tura yaro ya je ya koyi Al’kurani maimaikon neman kudi da malamai ke tura su a yanzu. Jibril ya ce a ckiin irin waddannan yaran ne Boko Haram ke dauka, su mayar da su mayaka.
Binciken da Kungiyar CDD ta yi ya nuna cewa akwai sakacin mahukunta wajen ilimantarwa akan tanadin yaki da 'yan ta'adda. Wani lauya mai zaman kansa da ya halarci taron, Rilwana AbdurRahaman, ya ce abinda ya hana kawo karshen wannan rikici na Boko Haram shine rashin yarda damahukunta suke nunawa, da kuma zargin cewa sun kashe mutanen dake zuwa suna tsegunta musu inda 'yan Boko Haram suke.
Ga cikakken bayanin yadda ta kaya a wannan taron a bakin Sule Mummuni Barma.
Facebook Forum