A yayin da sabuwar shekarar 2018 ke karatowa, wani masani mai fashin baki a kan al'amuran yau da kullum mazaunin kasar Ghana, Sheikh Usman Bari, ya ce akwai kalubale da dama da aka fuskanta a duniya gaba daya a shekarar 2017, musamman a fannin tattalin arziki da siyasa.
Sheikh Usman ya ce abin da ya fi daga hankali sosai shine barazanar da gwamnatocin Afrika suka fuskanta, kamar yadda aka sauke tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, kana da barazanar da Burkina Faso ta fuskanta da kuma zaben da aka yi a Liberiya.
Sheikh Usman ya kara da cewa akwai bukatar samarwa da matasa ayyukan yi domin dogaro da kai, yana mai cewa idan ba a yi haka ba, talauci zai yi katutu kuma za su rungumi miyagun halaye da ba'a bukata.
Ga cikakken bayani a rahoton da Ridwan Abbas ya aiko mana daga Ghana kan yadda ake auna shekarar nan mai karewa ta 2017.
Facebook Forum