Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Tayi Watsi Da Sukar Da Shugaban Amurka Yayi Mata


Shugaba Trump Na Amurka Da Takwaransa Xi Jingping
Shugaba Trump Na Amurka Da Takwaransa Xi Jingping

Kamar yadda Rasha ta yi watsi da manufofin Shugaba Trump na Amurka akan sabuwar manufar tsaron kasa da ya gabatar a jiya Litinin 18 ga watan Disambar shekarar nan ta 2017, haka ita ma Kasar Sin ta yi fatali da manufofin da suka jefata cikin wadanda suka zama barazana ga Amurka.

Kasar China tayi watsi da sukar lamirinta da Shugaba Donald Trump yayi a cikin sabuwar manufar tsaron kasarsa da ya gabatar, inda manufar ta ayyana China a zaman abokiyar adawa kuma kalubale ga akidojin Amurka.

Sabuwar manufar ta Trump ta soki lamirin shugabannin jam’iyyar Kwaminisanci ta China tare da zarginsu da kokarin yada tsarinsu na mulkin danniya a duniya da ma satar fasahar wasu mutane da kuma yada tsarin tattalin arzikinta da gwamnati ke kanainayewa.

Manufar ta bayyana wasu abubuwa guda uku da ke yin barazana ga zaman lafiya da kuma akidojin Amurka, baya ga kasashen Iran da Koriya ta Arewa da kuma kungiyoyin ta’addanci a duniya.

Manufar ta Amurka ta nuna China da Rasha a zaman manyan kasashen da ke kokarin shimfida wasu akidoji da muradu wadanda suka sha bamban da na Amurka a fadin duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG