Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Damke Fursunonin Da Suka Tsere A Akwa Ibom


Dan Sandan Najeriya
Dan Sandan Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce sun kama tare da mayar da fursunonin da suka tsere daga gidan yari a Ekot Ekene.

Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Akwa Ibom, Shuaibu Mu'azu yace an gano wasu fursunonin da suka balle daga gidan yarin da ke Ekot Ekene, an kuma mayar da su gidan yari.

Shu'aibu ya bayana cewa, babbar barazana ce ga harkar tsaro ace wadanda ake tsare dasu sun tsere, musamman ma fursunonin da aka dauresu akan manyan laifuffuka kamar fashi da makami da kisan kai da fyade da dai sauransu.

Kwamishinan yace za su yi aiki da duk wadanda zasu iya taimakawa wajen dakile wannan matsalar, ya kuma bukaci hadin kan al’umma wajen gano sauran fursunonin da ba a gano su ba bayan tserewar tasu.

A bangarensa, shugaban gidan yarin Akwa Ibom Mr Alex Odeta, ya bada umarnin yin bincike akan dalilan da ke jawo fursunoni suna ballewa daga gidan yari, duk da cewa akwai zargin cinkoso, da jiran shari’a ga wasu fursunonin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG