Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Somaliya Da Sojojin Amurka Sun Kashe Shugaban Al-Shabaab


Mayakan Al-Shabab
Mayakan Al-Shabab

"An tabbatar da cewa an kashe Maalim Ayman ne a wani farmakin hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya tare da taimakon sojojin Amurka suka yi a ranar 17 ga watan Disamba," in ji Daud Aweis a shafinsa na X da yammacin ranar Alhamis.

Dakarun Somaliya da na Amurka sun kashe wani babban jigo na kungiyar IS ta Al Shabaab wanda ke shirya kai hare-hare da dama a Somaliya da Kenya, in ji ministan yada labaran Somaliya.

"An tabbatar da cewa an kashe Maalim Ayman ne a wani farmakin hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya tare da taimakon sojojin Amurka suka yi a ranar 17 ga watan Disamba," in ji Daud Aweis a shafinsa na X da yammacin ranar Alhamis.

"Ayman ne ke da alhakin shirye-shirye da gudanar da hare-haren ta'addanci da dama a Somalia da kuma wasu kasashe na kusa," in ji shi.

Jiragen sojoji
Jiragen sojoji

Rundunar sojan Amurka dake Afrika, wato AFRICOM, ta kai wani hari ta sama in ji kakakin AFRICOM, amma ya kara da cewa har yanzu ba a tabbatar da takamamman inda aka kai harin ba.

Rundunar AFRICOM da ma'aikatar yada labaran Somaliya ta sanar da cewa an kai harin ne kan 'yan ta'addar a kusa da garin Jilib a kudancin Somaliya.

Ayman yana cikin jerin sunayen Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da ake nema ruwa a jallo, tare da bayar da tukuicin dala miliyan 10 ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga kamo shi.

Ma'aikatar ta ce shi ne ke da alhakin harin da aka kai a sansanin soji a Kenya a watan Janairun 2020 inda aka kashe Amurkawa uku.

~Rueters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG