An haifi Kabiru Usman Fagge ne a Kano, a ranar 12 ga watan Satumban shekarar 1946.
A shekarar 1956 ya shiga makarantar Firamare ta Fagge a kano, kuma a shekarar 1969 ya kamala karatun midil a Kuka Siniya. Ya wuce zuwa Kolejin Horas da Malamai ta Bichi inda ya shekara uku, sannan ya kammala a Kolejin horas da malamai ta Kano, KTC a shekarar 1970, inda ya sami takardar shaidar koyarwa mai daraja ta biyu (Grade 2).
Daga shekarar 1971-74, ya yi aikin koyarwa a makarantar Firamare ta Tudun wada da ke birnin Kano, sannan ya koma karo karatu a Jami'ar Bayero (ABU).
Bayan ya sami Digirinsa na farko a fannin Musulunci da tarihi, sai ya kama aiki a kamfanin wallafa Jaridun New Nigeria da Gaskiya Ta fi Kwabo.
Kabiru Usman Fagge, na daga cikin ma'aikatan farko da marigayi Audu Bako ya gayyato domin bude gidan Telibijin na Kano-Bompai a shekarar 1976.
Kafin ya kama aiki da Muryar Amurka, Alhaji Kabiru Fagge ya yi aiki a gidan telebijin na NTA Kano. Kafin nan kuma yayi aiki a kamfanin buga jaridun New Nigerian da kuma Hukumar Alhazai ta Nijeriya.
Yayin da ya ke tare da Sashin Hausa, Alhaji Kabiru Fagge ya yi aiki a matsayin mai gabatar da shirye-shirye, da karanta labarai. Daga cikin shirye-shiryen da ya gabatar akwai shirin "Ilimi Garkuwar Dan Adam" da "Sharhin Jaridun Amurka" da ya ke gabatarwa kowanne mako.
Marigayi Kabiru Fagge ya yi aiki da Sashen Hausa na Mauryar Amurka daga watan Yuni 1989, zuwa watan Yuni 2014 lokacin da ya yi ritaya yana matsayin babban Edita
Za a yi Sallar Jana'izar shi gobe Asabar da karfe 12:15 na rana a masallacin Prince George Muslim Association (PGMA).
Alhaji Kabiru Fagge ya rasu ya bar matarshi, 'ya'ya, da kuma jikoki.
Dandalin Mu Tattauna