Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sashin Doka Na 99 Na Iya Matsin Lambar Tsagaita Barin Wuta A Gaza


Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

Yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare da ya yi sanadiyar karuwar asarar rayukan fararen hula, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a yi amfani da wani karfin ikon da ba kasafai ake amfani da shi ba a wannan makon.

Guterres ya yi hakan ne don ya gargadi Kwamitin Sulhu kan "mummunan bala'i" da ke gabatowa a Gaza.

Ya bukaci membobin da su bukaci a tsagaita bude wuta bisa dalili na jinkai cikin gaggawa.

Guterres ya yi amfani da Sashin Doka Na 99 ko kuma Article 99 na Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya wanda ya ce zai iya sanar da majalisar batutuwan da ya yi imanin na barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa.

Sashin Doka Na 99 zai ba da ƙarin iko mai mahimmanci ga babban sakataren, tun da ainihin ikon da ke cikin Majalisar Dinkin Duniya na da kasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniya musamman kasashe 15 da ke cikin Kwamitin Tsaro.

Ba a cika amfani da Sashin Doka Na 99 ba. Lokaci na karshe da aka yi amfani da shi a yayin yakin da aka yi ne a shekarar 1971 wanda ya kai ga kirkiro Bangladesh da kuma raba kasar daga Pakistan.

Guterres ya nemi yin amfani da Sashin Doka Na 99 ne saboda yana ganin halin da ake ciki a Gaza yana cikin "mummunar hadarin rugujewa." Ya na ganin wani mataki ne da ya kamata a dauka.

Daular Larabawa, wakilin Larabawa a kwamitin sulhun, ta mika wani gajeren kuduri ga mambobin kwamitin sulhun a yammacin Larabar inda ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa. Yanzu haka suna shirin jefa kuri'a a taron kwamitin tsaro a yau Juma'a.

Amurka, wacce ita ce kawa mafi kusa ga Isra'ila kuma ke da ikon fada-a-ji kan kudurori, ba ta goyi bayan tsagaita wuta ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG