Satar mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya kuma a baya ma an sha kai wa ma'aikata 'yan kasashen waje hare-hare daga kungiyoyin ‘yan bindiga, musamman ma ma’aikatan hakar ma'adinai ko gine-gine.
Lamari na baya-bayan nan ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata a kan titin Ahoada da Abua, shiyyar Gabas da Yamma a kudancin jihar Rivers, in ji ‘yan sanda.
Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, maharan sun yi wa ayarin motocin da ke dauke da ma’aikatan Daewoo biyu kwanton bauna da misalin karfe 9:30 na safe.
‘Yan bindigar sun kwashe makaman sojojin.
‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da ‘yan Koriya biyu kafin suka gudu daga wurin,” in ji jami’in da bai so a bayyana sunansa ba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe Koko ta tabbatar da faruwar lamarin amma taki bada cikakken bayani.
"Muna kan binciken kan lamarin. Za mu ba ku cikakken bayani nan gaba," kamar yadda ta shaida wa AFP.
Har yanzu dai rundunar soja ko kamfanin Daewoo na Koriya ta Kudu ba su ce uffan kan harin ba.
Kamfanonin Asiya da dama da suka hada da China da Koriya ta Kudu suna aiki a Najeriya kuma galibi suna aikin gina tituna da layin dogo na kasar.
An sha garkuwa da wasu daga cikin wadannan ma’aikatan don neman kudin fansa a baya. Akan sakin ma’aikatan bayan an biya kudin fansa.
Dandalin Mu Tattauna