Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SEC Ta Tuhumi Shugaban Kamfanin Tingo Group Na Najeriya Da Damfara


 Dozy Mmobuosi
Dozy Mmobuosi

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar Kula da Hada-Hadar Kudi ta Amurka (SEC) ta gurfanar da dan kasuwan nan na Najeriya Dozy Mmobuosi da wasu kamfanoni uku wanda shi ne shugabansu, inda ake zargin su da damfarar masu zuba jari.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta SEC ta fitar ta ce ta shigar da kara a gaban kotun Amurka da ke New York a kan Mmobuosi, saboda ‘dan kasuwan ya yi shekara da shekaru yana karyar cewa kamfaninsa ya mallaki miliyoyin da bai da su.

SEC ta yi zargin cewa, tun akalla 2019, Mmobuosi ya karyata bayanan kuɗi da sauran takaddun kamfanoni uku da rukuninsu na Tingo Mobile da Tingo Foods.

Kamfanoninsa uku; Tingo Group Inc., Agri-Fintech Holdings Inc. da Tingo International Holdings Inc suna cikin wadanda ake tuhuma.

Hukumar ta SEC ta ce Dozy Mmobuosi yana yin hakan ne saboda ya yaudari masu hannun jari a fadin duniya, don haka za a hukunta shi.

Tingo ya musanta dukkan zarge-zargen da aka yi na rahoton, yana mai cewa yana cike da "karya da batanci".

SEC ta sanya dokar dakatar da ciniki na tsawon mako biyu na kasuwancin Tingo Group a ranar 14 ga Nuwamba biyo bayan binciken.

NASDAQ ya ba da shawarar cewa za ta ci gaba da kiyaye amincin kamfanin har sai an sake nazari, in ji Tingo Group a cikin wata sanarwa.

Ba a iya samun Mmobuosi da kamfanonin don jin ta bakinsu ba amma Tingo Group a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo ta ce za ta ba da cikakken hadin kai ga masu gudanar da bincike.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG