Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife Ya Rasu Yana Da Shekara 85


Chukwuemeka Ezeife
Chukwuemeka Ezeife

Dokta Chukwuemeka Ezeife, wanda jigo ne a kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo, ya rasu ne a babban asibitin Tarayya da ke Abuja a sakamakon rashin lafiya.

An bayyana rasuwarsa cikin wata takaitacciyar sanarwar manema labarai da aka fitar a yau Juma'a da safe, 15 ga watan Disamba mai dauke da sa hannun Cif Rob Ezeife a madadin iyalin.

Sanarwar kamar yadda The Cable ta rawaito ta ce:

"A madadin Iyalan Ezeife na Igbo-Ukwu, ina son sanar da rasuwar babban dan mu, 'Okwadike', Dakta Chukwuemeka Ezeife, CON, tsohon sakataren dindindin, tsohon gwamnan Jihar Anambra, tsohon mashawarcin shugaban kasa kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa. "Abin bakin cikin ya faru ne jiya misalin karfe 6 na yamma a Cibiyar Lafiya, Abuja. "Za a fitar da karin bayani dangane da marigayin da shirye-shiryen birne shi nan gaba."

Chukwuemeka Ezeife tsohon mashawarcin shugaban kasa ne, kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG