Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken Zai Kai Ziyara Kasashen Cabo Verde, Ivory Coast, Najeriya, Da Angola daga 21 zuwa 26 ga watan Janairu, 2024.
A yayin ziyarar, Sakataren zai yi tsokaci kan yadda Amurka ta kara inganta hadin gwiwar Amurka da Afirka tun bayan taron Shugabannin Amurka da Afirka, da suka hada da yanayi, abinci, da kiwon lafiya.
Har ila yau, zai jaddada dangantakarmu ta fuskar tattalin arziki a nan gaba, da yadda Amurka ke zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a nahiyar Afirka, domin bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin juna, da samar da ayyukan yi a gida da ma nahiyar, da taimakawa Afirka ta yadda za ta iya takara a kasuwannin duniya.
Bugu da kari, Sakataren zai ci gaba da hadin gwiwar tsaro bisa dabi'u iri daya kamar mutunta 'yancin dan Adam, inganta dimokradiyya, da fadada tsarin doka.
Zai kuma jaddada aniyar Amurka ga abokan huldar kasar da ke yammacin Afirka ta hanyar dabarun hana tashe-tashen hankula da samar da zaman lafiya, da hadin gwiwar Amurka da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) don magance kalubalen yankin, da kokarin Amurka na tallafawa shugabannin Afirka wajen dakile ta'addanci, tashe-tashen hankula da daukar matakan diflomasiyya kan rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango.
Amurka ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da hulda tsakanin Amurka da Afirka.
Dandalin Mu Tattauna